
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon Gwamnan Jihar Anambara kuma tsohon Ministan Ƙwadago da Ayyuka, Dakta Chris Ngige, ya shiga hannun Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) bisa zargin sa da ayyukan da ke da alaƙa da cin hanci da rashawa.
Tsohon hadimin Ngige mai suna Fred Chukwulobe ne ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce jami’an EFCC sun kama tsohon ministan ne domin amsa wasu tambayoyi kan waɗansu kuɗaɗe da ake zargin an karkatar da su lokacin da yake kan muƙami.
Kodayake hukumar EFCC ba ta fitar da cikakken bayani ba tukuna, amma ana sa ran za ta bayyana dalilin tsarewar nan ba da jimawa ba.
Chukwulobe ya kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa an yi awon-gaba da Ngige wanda ya yi minista a zamanin mulkin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a lokacin da wasu ƴan bindiga suka farmaki tawagar motocinsa a Anambara. An gano cewa al’amarin ya faru ne a lokacin da Ngige baya nan.
