2027: A shirye muke mu fitar da nagartattun ‘yan takara a APC – Injiniya Bichi

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Bichi, a Nijeriya Engr. Abubakar Kabir Bichi ya ce APC za ta fitar da nagartattun ƴan takara a 2027.

A jawabin da ya yi lokacin da jagororin siyasar Ɓagwai da Shanono suka kai masa ziyara a Abuja, Engr Bichi ya ce lokaci ya yi da jam’iyyar APC za ta ƙara tsari da tantancewar ƴan takara masu nagarta.

Ya bayyana cewa hakan ne zai taimaka wajen tabbatar da karɓuwa da samun nasara a babban zaɓen 2027, musamman a Kano da Arewa baki ɗaya.

Kazalika Engr Abubakar Kabir Bichi ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai a jam’iyyar APC a Kano, inda yayi kira ga magoya baya da su ci gaba da mara wa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu baya domin tabbatar da cigaban Najeriya da nasarar APC a matakai daban-daban.

By ukarofi