Remi Tinubu ta magantu kan cece-kucen taƙaddamarta da gwamnan Osun

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Matar Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta warware batun taƙaddamar da ta faru tsakanin ta da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke a taron cikar Ooni na Masarautar Ife, Adeyeye Ogunwusi shekaru 10 a kujerar sarauta.

A wani bidiyo da ya karaɗe kafafen watsa labarai a ranar Litinin, an ga yadda Adeleke ya je kan mimbari da nufin yin jawabin taya murna ga matar shugaban ƙasar bisa karrama ta da sarautar ‘Yeye Asiwaju Gbogbo Ile Oodua’.

A madadin haka ne sai gwamnan ya soma abin da ya saba na ƙoƙarin nishaɗantar da jama’a gabanin jawabinsa na taro, wanda mutane da dama a wajen suka nuna jin daɗinsu a kai.

Ganin haka ke da wuya sai Sanata Remi, bayan karɓar naɗin da aka mata, ta je kusa da shi, sannan ta yi masa raɗar cewa ya cigaba da jawabinsa.

Wannan al’amari ya janyo cece-kuce acikin al’ummar Nijeriya ciki har da Mai taimaka wa gwamnan akan al’amuran hidimar al’umma, Akintunde Bello, wanda ya ce kawai buƙatar a ƙalubalence ta akan haka.

Da take tsokaci akan lamarin ta shafin Facebook bayan ɗora hotonta tare da gwamnan, Remi ta ce babu wani abin faɗi-in-faɗa acikin abin ta aikata, saboda waɗanda aka ba shugabancin al’umma, an yarda cewa za su sauke nauyin da aka ɗora musu bisa tsari.

Don haka ta ce, masu kururuta al’amarin suna yin haka ne don suka da ƙoƙarin mayar da abinda ba abin magana ba cece-kuce.

To saidai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, babu wani saƙo daga gwamnan na Osun akan al’amarin.

By Babaji