EFCC ta ci gaba da riƙe Malami kan binciken alaƙanta shi da asusun bankuna 46

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Antoni Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya shafe kwana na biyu a tsare a hannun Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) bayan kasa cika sharuɗɗan belinsa.

Majiyoyi sun ce ana bincikensa ne akan zarge-zargen laifuka 18, ciki har da hada-hadar kuɗi da saɓa ka’idar aikin ofis, da kuma zargin taimaka wa ayyukan ta’addanci ta hanyar kuɗi.

Haka kuma, ana tuhumar sa kan yadda aka yi asarar Dala miliyan 346.2 na kuɗin Abacha da aka dawo da su daga Switzerland da Jersey, da kuma rabon kuɗaɗen shirin Anchor Borrowers na Naira biliyan 4.

EFCC na kuma binciken zargin cewa Malami ya zuba Naira biliyan 10 a makarantu, otal-otal da injinan shinkafa a Kebbi, tare da duba akalla asusun banki 46 da ake zargin suna da alaƙa da shi.

Malami, wanda ya koma jam’iyyar ADC a 2025, ya bayyana aniyarsa ta takarar gwamnan Kebbi a 2027, a wani yunƙuri na ci-gaban siyasarsa.

Rahotanni sun bayyana wasu manyan mu’amaloli biyar da ake zargin sun faru a lokacin da Malami ke ofis, ciki har da biyan Dala miliyan 496 ga GSHL a batun Ajaokuta, da sayar da kadarorin da aka ƙwace, da kuma rikicin biyan Dala miliyan 419 ga masu neman diyya na Paris Club.

By Babaji