
Dakarun Rundunar 8 ta Division ta Nijeriya a Sakkwato, sun samu gagarumar nasarar kawar da fitaccen shugaban ƴan bindiga, Kachalla Kallamu, a yankin Ƙaramar Hukumar Sabon Birni.
An kashe Kallamu ne a wani samame na musamman da sojoji suka gudanar tare da haɗin-gwiwar ƴan sa-kai a yankin Kurawa da safiyar ranar Litinin.
Kallamu, wanda babban na hannun daman shugaban ƴan bindiga Bello Turji ne, ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka addabi al’ummar Sabon Birni da hare-hare, garkuwa da mutane da kuma tada tarzoma a yankin.
Rahotonni sun bayyana cewa an kashe shi ne tare da ɗaya daga cikin manyan masu samar wa Turji da kayan aiki da bayanan sirri, a wani artabu da ya faru a ranar tare da wasu tarin ƴan bindiga.
Haka kuma, rahotannin sun ce Kallamu, wanda asalinsa ɗan Garin-Idi a Sabon Birni ne, ya dawo ne cikin yankin bayan tsere wa wani farmaki da sojoji suka kai masa a watan Yunin 2025, inda ake zargin ya shige kogi domin neman mafaka.
