
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanannen jarumin fina-finan masana’antar Kannywood kuma daɗaɗɗen furodusa, Hamisu Lamiɗo Iyantama, ya samu lambar girmamawa a taron baje kolin fina-finai na ƙasa-da-ƙasa, wato Zuma International Film Festival, wanda Hukumar Kula da Fina-finai ta ƙasa (NFC) ta shirya.
Taron, wanda aka gudanar a birnin tarayya Abuja a yau Laraba, ya jinjina wa gudumawar da Iyantama ya bayar a harkar fim musamman duba da yadda ya shafe tsawon shekaru da dama aciki, lamarin da ya taimaka wa ci-gaban fannin da ma masana’antar fim ta Arewa a keɓance.
Da yake jawabi a taron, Iyantama ya miƙa godiyarsa ga hukumar musamman ƙarƙashin jagorancin Dakta Ali Nuhu, wanda shi ne ɗan fim na farko da ya taɓa riƙe muƙamin.
Iyantama ya ce, wannan shi ne karo na huɗu da hukumar kula da fina-finan take karrama shi, inda a 2018 ya samu kyautar karramawa ta fim ɗinsa mai suna Tsintsiya, wanda ofishin jakadancin Amurka a Abuja ya ɗauki nauyi.
A shekarar ne hallau NFC ta ɗauki nauyin tafiyarsa zuwa Los Angeles da Santa Monica domin halartar taron baje kolin fina-finan Amurka, wato ‘American Film Market, wanda shi ne mafi girma a duniya.
Daga bisani an kuma karrama daɗaɗɗen jarumin da kyautar Hall of Fame a Legas, lamarin da ya sa shi sahun mutanen da suka yi fice a fanninsu.
A ƙarshe, Iyantama ya yi godiya ga Ali Nuhu, waɗanda suka shirya taron, abokan aiki, iyalansa da magoya bayansa bisa gudunmawarsu da suka taimaka masa wajen kai wa matakin da ya tsinci kansa a ciki.




