Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Tsofaffin shugabannin Hukumar Hisbah ta Jihar Kano sun bayyana matsayinsu kan batun kafa wata sabuwar hukumar Hisbah mai zaman kanta, inda suka nuna cewa ba za su amince da hakan ba, tare da gargaɗin cewa bai kamata a siyasantar da hukumar ba.
Sun bayyana wannan matsaya ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ɗakin taron Cibiyar ‘Yan Jarida ta Jihar Kano ranar Alhamis.
Da yake jawabi a madadinsu, Farfesa Mai Bushira, ya ce an samu rahotannin cewa an sallami wasu jami’an Hisbah ba tare da bin ƙa’ida ba, lamarin da ya haifar da damuwa.
Farfesa Mai Bushira ya ƙara da cewa “Mun samu rahoton cewa an sallami wasu jami’an Hisbah ba bisa ƙa’ida ba. Wannan abu ne da zai iya haifar da rikice-rikice a cikin tsarin hukumar. Ba za mu yarda a kafa wata sabuwar Hisbah da za ta kawo rashin daidaito ba.”
Tsofaffin shugabannin Hisbah ɗin sun ce hukumar ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ɗa’a, tsaro, da inganta tarbiyyar al’umma, don haka ya zama wajibi gwamnati ta yi duk mai yiwuwa wajen tallafa mata.
Kazalika sun yi kira ga gwamnatin Jihar Kano da ta samar wa Hukumar Hisbah kayan aiki na zamani, da kuma magance duk wata matsala da ke damunta cikin gaggawa, domin ƙarfafa ayyukanta da tabbatar da cewa tana ci gaba da aiki yadda ya kamata.
A cewarsu, duk wani yunƙurin siyasantar da Hisbah ko samar da wata sabuwar hukuma mai zaman kanta zai iya kawo ruɗani da rushewar tsarin da aka gina tsawon lokaci.
Sun kuma roƙi gwamnati da shugabanni su mutunta darajar hukumar Hisbah, tare da yin duk mai yiwuwa don kare martabar ta da tabbatar da ci gabanta a jihar Kano.
