Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya zargi manyan ‘yan siyasar Nijeriya da gaza yi wa ƙasa aiki, yana mai cewa suna naushin cigaban al’umma ta hanyar fifita kansu a kan buƙatun jama’a.
Sarkin na wannan jawabi ne a bikin cika shekaru 15 da kafuwar Enough is Enough (EiE) Nigeria a Lagos, ranar Laraba, Sanusi ya bayyana cewa Nijeriya na ci gaba da rasa muhimman damar bunkasuwa saboda yadda wasu ke ɗaukar muƙaman gwamnati a matsayin “gadon gidansu” amanar al’umma ba.
A cewarsa, yawancin shugabannin siyasa suna sa buƙatunsu da na iyalansu a gaba fiye da muradun ƙasa.
“Mun yi wa ƙasar nan barna sosai, kuma lokaci ya yi da za mu dakata,” inji tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya.
“Ba wai damar da ta wuce kawai ba sai ma wacce aka bari da gangan. Matsalar ita ce muna da mutane da ke ganin kujerar gwamnati mallakinsu ce da ta iyalansu, alhali kuwa ita ce amanar ’yan ƙasa.”
Kazalika Sanusi ya buƙaci matasan Nijeriya da su ƙaurace wa tsarin mulki mara inganci da suka gada, tare da dagewa wajen gina kasa mai haɗa kan jama’a da tsayayyen hangen cigaba.
Ya kuma gargaɗi cewa tsarin siyasa na yanzu, wanda ya ta’allaka kan “bambancin ƙabilu, rikice-rikicen addini da son zuciya,” ba zai taɓa samar da cigaban da ake buƙata ba.
“Muhimmiyar magana ita ce, mu ’yan ƙasa mu tuna Nijeriya tamu ce. Ba mallakin gwamnati ba ce, ba mallakin ’yan siyasa ba ce,” inji shi.
Sannan ya ƙara da cewa, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su haɗa kai wajen samar da sabuwar aƙida da manhajar jagoranci mai amfani wa ƙasa gaba ɗaya.
“Mu ne mallakin wannan ƙasa, kuma duk inda muka tsinci kanmu, ya kamata mu taka rawar gani. Abin da muke buƙata shi ne hangen nesa mai tsafta da za a iya aiwatarwa game da irin Nijeriya da muke so—wacce ta bambanta da wadda aka tilasta mana,” a cewarsa.
Sanusi ya ƙarkare da cewa, da cewa haɗin kan jama’a da kishin ƙasa ne kaɗai zai iya fito da Nijeriya daga halin da take ciki zuwa ƙasar da za ta taka rawar gani a duniya.
