Daga JAMIL GULMA a Kebbi
A duk lokacin da mutane biyu ko fiye da haka suke neman abu ɗaya kuma ba za a iya raba shi ba, to ba shakka kowane cikionsu yana iya yin duk yadda zai yi ya kai gaci, don haka ba shakka akwai gumurzu.
Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Kebbi tana kusa tsunduma cikin rikicin cikin gida da ke iya kai ta ga rugujewa, saboda a kullum ’yan takarar neman makamai daban-daban tun kama daga majalisar dokoki ta jiha zuwa Majalisar Wakilai ta Tarayya sai bayyana su ke yi daga sassa daban-daban na jihar, inda kowane kuma yana iya ɗaukar kowane mataki, don cimma muradinsa.
Waɗansu suna ta faman kamun ƙafa ga Gwamna Nasir Idris, waɗansu kuma suna amfani da dangantakarsu da matan gwamnan yayin da kuma waɗansu suna amfani da aljihunsu wajen shirya talllafi daban-daban ga mutanen yankinsu, saboda neman a yaɗa manufofinsu bisa ga la’akari da kyauta tana daga cikin halayen Gwamna Malam Nasir kuma yana son mutane masu kyauta da taimakon mutane.
Yanzu haka dai duk waɗannan ’yan takarar kowane ya ja daga da shi da ’yan bangarsa da ’yan soshiyal midiya nasa suna ta tallata shi tare da harbin abokan hamayya a fili ko a fakaice ta hanyar rubuce-rubuce a shafukkan kafafen sada zumunta daban-daban da kuma zahiri a wuraren tarukan bikin suna ko daurin aure wani lokacin har ma wajen zaman karbar gaisuwar mutuwa.
Tsohon Gwamnan Jihar Kebbi kuma tsohon sanatan gundumar Kebbi ta Tsakiya, Sanata Atiku Abubakar Bagudu, wanda shine Ministan Kasafi da Tattalin Arziki na Nijeriya da yanzu haka yana hararen sake ɗare kujerar sanatan gundumar Kebbi ta Tsakiya da Sanata Adamu Aliero ke kai a halin yanzu a zaɓen shekarar 2027 idan Allah ya kai mu duk da akwai maganar shugaban ƙasa ya ba sanatocin Kebbi damar zarcewa kai tsaye.
Waɗansu bayanai daga makusantan Sanata Atiku Abubakar Bagudu sun bayyana cewa, suna nan kan ƙudirinsu na neman kujerar sanatan gundumar Kebbi ta Tsakiya, saboda babu wata hujja da za ta sa a hana shi takara tun da babu wata doka ko dai ta Jam’iyya ko kuma ta Kundin Tsarin Mulki.
Majiyar ta bayyana cewa, da ma dangantaka tsakanin Sanata Adamu Aliero da Sanata Atiku Bagudu ta daɗe da tsami, inda a kwanan baya a wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sai da aka yamutsa gashin baki inda daya aka soma bayyana cewa, Sanata Atiku Bagudu yana kurarin Malam Nasir da wahala ya kawo jihar a zaɓen shekarar 2027, saboda ba shi da wata ƙwarewa a wajen gudanar da mulki.
Kuma aka shawarci Gwamna Malam Nasir Idris da ya kamata ya ƙara nasa deleget-deleget da esko-esko, saboda waɗanda ke nan a halin yanzu ba nasa ba ne yana kan shimfiɗar waɗansu mutane ne da ke da shirin yi masa ko ta kwana yayin tsayar da ’yan takara, don zaɓen shekarar 2027.
A gundumar Kebbi ta Arewa ma yanzu haka tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Hon. Hussaini Suleman Zango Kangiwa (Yan Tagwayen Kangiwa) shi ma yana neman kujerar ɗan Majalisar Dattawa mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa da Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi tsohon shugaban masu rinjaye ke akai duk da sanin cewa, an riga an tabbata Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi zai yi sake tsaya wa takarar kujerar a karo na huɗu.
Har wa yau dai a cikin masu son takarar kujerar ɗan Majalisar Dattawa a Kebbi ta Arewa akwai tsohon Gwamnan Kebbi Alhaji Saidu Usman Nasamu ɗakingari daga ƙaramar Hukumar Suru, wanda bayan kammala wa’adinsa na gwaman jihar a shekarar 2015 ya nemi kujerar, amma sai dai bai sami nasara ba, inda Sanata Yahaya ya kada shi.
Sai dai Hausawa kan ce “abin kamar da wuya”, saboda kujerar Sanatan gundumar Kebbi ta Arewa mallakar masarautar Kabin Argungu ce, amma saboda tana da ƙananan hukumomi huɗu ne kacal, don haka sai aka ɗebo ƙananan hukumomin Suru da Bagudo suka zama shida, saboda haka su waɗannan ƙananan hukumomin Suru da Bagudo an yi amfani da su ne a matsayin ’yan cikon giɓi ne, don haka sanata ba zai taɓa fitowa daga waɗannan ƙananan hukumomin ba duk da kasancewar suna daga cikin gundumar Kebbi ta Arewa.
Haka zalika a gundumar Kebbi ta Kudu akwai raɗe-raɗen hana Sanata Garba Maidoki takara sanadiyyar rashin jituwar da ke tsakaninsu da Gwamna Nasir Idris wacce ta ƙara ƙamari lokacin da Sanata Maidoki ya goyi bayan jami’an tsaro da suka bar harabar makarantar GGCSS Maga har ’yan bindiga suka zo suka sace ɗalibai 25 suka yi garkuwa da su, inda ya ce suna aiki ne da umarni kuma su ’yan bindigar sun fi ƙarfinsu, wannan shi ne dalilin da ya suka bar wajen.
Yayin da shi kuma Gwamna Nasir Idris ya ƙeƙasa ƙasa ya ce, lallai sai an bayyana dalilin ba su umarnin barin harabar makarantar duk da irin rahotannin da suka samu na cewa akwai yiyuwar a kai farmaki a makarantar, saboda haka suka ɗauki matakin kai jami’an tsaro.
Yanzu haka dai akwai fargabar tarihi ya maimaita kan sa ga Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Kebbi, saboda ga yadda ’yan siyasa masu neman mukamai ke tururuwa suna shiga jam’iyyar, amma da ƙafa biyu, saboda mafi yawancinsu idan ba su sami biyan buƙata ba za su canja sheka zuwa Jam’iyyar adawa ta ADC mai tasowa, wacce yanzu haka ake zargin a asirce manyan jami’an gwamnati da ’yan siyasa suna nan suna mubayi’a da zummar idan aka yi babban taron Jam’iyyar APC kowa ya san matsayinsa su kuma a nan ne za su ɗauki mataki.
Yanzu dai abin jira shi ne sai lokacin da aka yi babban taron APC ko ma menene zai faru.
