Ƙudurin sake fasalin dokokin haraji

Spread the love

A wani lokaci da tattalin arzikin ƙasa ke buƙatar daidaito, gaskiya da tsarin da ya dace, gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta ɗauki mataki mai nisa wajen sake fasalin dokokin haraji domin farfaɗo da tattalin arziki da kuma dawo da amincewar jama’a ga yadda ake gudanar da haraji a Nijeriya. Wannan sabon tsarin, wanda zai fara aiki a 2026, wani babban lamari ne da ya tsaya kan gaskiya, sauƙi da kare al’ummar ƙasa — musamman masu ƙaramin ƙarfi.

A karin gaskiya, tsarin haraji a baya ya yi nauyi ga ‘yan kasuwa, ya ƙara ruɗani ga zuba jari, ya hana yawancin mutane fahimtar abin da ake karɓa da abin da ake kashewa. Tsarin da gwamnatin Tinubu ta kawo yanzu ya fito da wani sabon salo na ƙwarewa, bayyananniyar hanya da kuma kawar da ruɗani wanda ya daɗe yana ci wa mutane tuwo a kwarya.

Shugaban kwamitin aiwatar da tsarin, Joseph Tegbe, ya yi magana da harshen gaskiya — cewa gwamnati ba za ta cutar da jama’a ba, kuma ba a kawo wannan tsarin domin tsananta haraji ko wawure aljihun talaka ba, sai dai domin daidaita ɗabi’ar tattara kuɗaɗen shiga ta hanyar da ta dace da zamani. Wannan shi ne abin da ƙasashen da suka ci gaba suka yi shekaru da dama kafin su cimma daidaito.

A yau, Nijeriya na fuskantar manyan ƙalubale: ƙarancin kuɗaɗen shiga, hauhawar farashi, da takurawar tattalin arziki. Wannan sabon tsarin haraji shi ne ginshiƙin da za a iya ɗora sabuwar tattalin arzikin da ake hanƙoron ginawa — tattalin arzikin da ke rage jinkiri tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa, da kuma bai wa masu zuba jari kwarin gwiwa.

Kwamitin ya kuma tabbatar da cewa tsarin zai kare masu rauni, zai rage rashin tabbas ga ‘yan kasuwa, kuma zai fayyace dokoki tsakanin jihohi da Tarayya. Wannan babban ci gaba ne da ya dace da ƙasa mai jama’a fiye da miliyan 200 da ke buƙatar tsari guda, mai ma’ana da inganci.

A fili yake cewa gwamnati ba ta shigo da wannan sabon tsarin domin harin bankuna ko shiga bayanan mutane ba — wannan tsoro kuwa an kawar da shi a fili. Gwamnati ta yi bayani a sarari cewa babu wata niyya ta danniya ko cin zarafin sirrikan jama’a. A maimakon haka, an gina tsarin ne bisa adalci da kare haƙƙin masu biyan haraji.

Game da rikicin Capital Gains Tax (CGT), gwamnatin Tinubu ta nuna cewa tana sauraron jama’a, tana gyara matsaloli, tana duban damuwa, kuma tana da niyyar daidaita duk wani sashi da zai iya cutar da harkokin kasuwa. Irin wannan sassauci shi ne ainihin ma’anar shugabanci na zamani.

Idan aka yi la’akari da cikakken tasirin wannan sabon tsarin, za a ga cewa Nijeriya na kan hanyar gina sabuwar gada tsakanin gwamnati da al’umma ta hanyar bayyana gaskiya: ƙasar da ke son hanzarta ci gaba, dole ne ta samar da tsarin haraji da ke da hujja, tsari, da adalci.

Shugaba Tinubu da tawagarsa sun yi nisan da ba a jima an yi irinsa ba — matakin da ba wai kawai zai gyara haraji ba, har ma zai dawo da wani sabon hangen arziki ga tattalin arziƙin Nijeriya. Wannan aikin gyaran ya cancanci yabo saboda yana gina ƙasa mai nagarta, mai tsari, mai gaskiya da kuma mai mutunta ’yan ƙasa.

A ƙarshe, idan za a yi tarihi game da mulkin Tinubu a fannin tattalin arziki, wannan sabon tsarin haraji na iya zama ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan da suka nuna jajircewa, hangen nesa, da ƙudurin gina ƙasa mai ɗorewa ga ƙarni mai zuwa.

By ukarofi