Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Shugaban ƙaramar Hukumar Augie Honarabul Yahaya Muhammed Augie ya jaddada ƙudurinsa na bai wa yaƙi da cutar shan Inna da sauran cututtuka a ƙaramar Hukumar Augie.
Ya bayyana haka ne yayin ƙaddamar da allurar maganin cutar shan Inna a ƙaramar hukumar Augie ranar Litinin ɗin da ta gabata.
Alhaji Yahaya Muhammed Augie ya ya bayyana cewa fannin lafiya ba abin wasa ba ne musamman ga yara da mata masu juna biyu da kuma marasa galihu saboda su ne suka fi cancantar samun kulawa idan aka yi la’akari da yanayin da suka samu kan su, kun ko bayan wannan suna da haƙƙi na samun kulawar hukuma.
Ya kuma bayyana cewa ƙaramar hukumar Augie za ta baiwa ma’aikatar lafiya hadin kai da goyon baya a cikin shirin ta na allurar rigakafin maganin cutar shan Inna da sauran cututtuka don samun nasarar aikin ya isa kowane lungu da saƙo a faɗin ƙaramar hukumar Augie.
Ya yabawa jami’an kiwon lafiya bisa irin jajircewarsu a kan wannan aikin tare da alƙawarin bayar da kowace irin gudummawa don samun nasarar aiwatar da wannan aikin.
Ya kuma bayyana ƙudurinsa na haɗin gwiwa da ƙungiyoyi na masana a kan harkar lafiya da masu ruwa da tsaki domin fitowa da sababbin hanyoyi na daƙile duk wata hanya da ke iya haifar ɓarkewar wata cuta ta hanyar shirya gangamin wayar da kai don bayar da shawarwari ga magidanta.
