Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An gudanar da bikin rufe bajekoli na duniya Karo na 46 da Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Ambassada Usman Darma suka gudanar.
A yayin taron rufe bajekolin da aka gudanar a yammacin ranar Asabar ya samu halartar Sanatan Kano ta tsakiya Hon. Rufa’i Sani Hanga da Kwamishinan kasuwanci na jihar Kano Wada Sagagi. Haka kuma wakilai daga masarautun Kano da shugabannin cibiyoyin kasuwanci na jihohin Kaduna, Zamfara da Gombe da sauran hukumomin gwamnati da ‘yan kasuwa.
Da yake jawabi a yayin rufe taron shugaban cibiyar Kasuwanci da masana’antu na jihar Kano, Ambasada Usman Darma ya nuna matuƙar farin cikinsa bisa yadda aka soma bajekolin lafiya aka kammala lafiya cikin nasara.
Ya yi nuni da cewa cibiyar Kasuwanci ta Kano an kafata ne tun 1922 tana daga tsofaffin cibiyoyin kasuwanci a Nijeriya da ta shafe shekaru 100 tana gudanar da harkoki an fara bajekoli na farko ne a 1979 shekara 46 kenan.
Ya gode wa gwamnatin jihar Kano bisa muhimman ayyuka da ta aiwatar da suka bada kyakkyawan yanayi na haɓaka harkar kasuwanci kuma cibiyar na shirye da cigaba da haɗin gwiwa da gwamnatin jihar Kano don inganta tattalin arziƙi.
Ambassada Darma ya ce daga muhimman nasarori da aka samu a bajekolin na bana sun haɗa da sa hannun yarjejeniya tsakanin cibiyar da ƙungiyar ‘yan kasuwa ta ƙasar Ruwanda da ta ƙasar Ghana don haɓaka harkar kasuwanci sun kuma yi tattaunawa ta musamman da jakadan ƙasar Bangaladash don samar da zuba jari akan harkar roba da na wutar lantarki da kimiyya sun kuma tattauna da jakadan ƙasar Indiya don samar da damar zuba jari a fannin fasaha.
Ya ƙara da cewa sun kuma tattauna da wakilan hukumar da ke kula da harkokin jiragen ruwa NIMASA kan bunƙasa kasuwanci ta hanyar fito da jiragen ruwa sun kuma gana da jakadar ƙasar Sin don ƙarfafa kasuwanci da samar da horo a tsakanin ‘yan kasuwa na jihar Kano da na ƙasar Sin. Sun samu nasarar halartar jihohi da dama bajekolin musamman na Filato da Zamfara za su ƙara ƙulla hulɗar alaƙoƙi da su don bunƙasa tattalin arziƙi.
Ya ƙara da bayyana cewa a karon farko cikin tarihin kasuwar bajekolin ta gabatar da yin gasar nuna fasaha a tsakanin matasa domin gano zaƙaƙurai a cikinsu kuma a yayin gasar akwai Malam Ibrahim Abubakar wani mai buƙata ta musamman ya nuna fasaha ta ƙera mota ta kansa da aka gabatar a gasar ya samu nasarar zama na ɗaya cibiyar kuma ta tallafa masa da N1,000,000 dan ƙarfafa masa gwiwa sannan ya yi kira gwamnatin jihar Kano ta ƙara himma wajen bada kulawa ga yara masu fasaha don taimakawa wajen bunƙasa kimiyya da fasaha.
Ambassada Usman Dama ya ce cibiyar kasuwanci da masana’antu ta jihar Kano na shirin gudanar da muhimman abubuwa da suka haɗa da samar da banki na Microfinance don taimakawa ƙanana da matsakaitan ‘yan kasuwa akan harkar kasuwanci, sannan za ta samar da cibiyar horas da fasaha ta zamani a ɓangarori daban-daban don ƙara bunƙasa harkokin sana’a da tattalin arziƙi.
