Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Dattawa ta umurci Kwamitin Harkokin ‘Yan Sanda da ya gudanar da cikakken bincike kan zargin nuna wariya wajen aiwatar da umarnin Shugaba Bola Tinubu na janye jami’an tsaro daga gadin manyan mutane.
Wannan mataki ya biyo bayan ƙorafin da aka riƙa yi cewa wasu manyan mutane na ci gaba da amfani da ‘yan sanda, alhali ana cire na wasu ɓangarori musamman ‘yan majalisa, lamarin da ya tayar da ƙura a zaman majalisar ranar Laraba.
Sanata Abdul Ningi na Bauchi ta Tsakiya ne ya gabatar da batun a ƙarƙashin Dokar 9 ta majalisa, inda ya nuna mamaki da takaici cewa an janye masa ɗan sandan da ke masa rakiya, alhali ministoci, ‘yan kasuwa, iyalan manyan ‘yan siyasa da ma mawaƙa na ci gaba da yawo da tarin da ‘yan sanda.
Ningi ya jaddada cewa aiwatar da tsarin a bango guda – yayin da majalisa ake barinta a buɗe – na iya jefa ‘yan majalisa cikin haɗari, tare da karkatar da maƙasudin da shugaban ƙasa ya sa gaba wajen sake fasalin tsaron cikin gida.
Ya ce, “Idan za a janye tsaro, to a yi shi ga kowa. Na ga ministoci da dakaru, ‘yan kasuwa da na su, ‘ya’yan manyan ‘yan siyasa da na su, har ma mawaƙa da suke da cikakken tsaro. Amma Sanata a ce ba shi da ko guda ɗaya? Wannan ba ya faruwa a kowace dimokraɗiyya.”
Ya ce, baya adawa da tsarin shugaban ƙasa, muddin ana yi ne cikin gaskiya da adalci, ba nuna bambanci ba.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya tabbatar da cewa shugabancin majalisar ya tattauna batun tun kafin zaman, kuma an fara ɗaukar matakan warware damuwar ‘yan majalisa. Ya ce akwai alamun cewa umarnin shugaban ƙasa bai samu aiwatarwa daidai ba a ɓangarori daban-daban.
Jibrin ya ce, “Muna sa ran ganin martani dangane da janye ’yan sandan da aka ɗauka daga sanatoci. Me ya sa umarnin shugaban ƙasa zai zama abin kaucewa? Shugaban ƙasa ya bayar da shi ne cikin gaskiya don inganta aikin ‘yan sanda da tsaron cikin gida.”
Ya ƙara da cewa shugabannin majalisar sun amince cewa dole a dauki matakin gaggawa na dawo da jami’an tsaron sanatoci, tare da kwarin gwiwa cewa shugaban ƙasa zai saurari koke su.
