
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyoyin masu shirya fina-finai na MOPPAN da AFMAN sun yi ƙarin haske game da buɗaɗɗiyar saƙon da suka aike wa Hukumar kula da fina-finai ta ƙasa (NFC) sakamakon abin da suka kira da rashin fahimtar saƙonsu daga wasu mambobin masana’antar Kannywood da ɗaiɗaikun al’umma.
A wata takarda da ƙungiyoyin suka fitar mai ɗauke da sanya hannun Shugabannin MOPPAN da AFMAN, wato Shehu Hassan Kano da Salisu Mohammed Officer, sun ce kwatakwata ba su da nufin kushe ko kai farmaki ga jagorancin Darakta Manaja na NFC, wato Dakta Ali Nuhu.
A cewarsu, ƙorafi suka yi akan yadda ake sakaci da al’amuransu da ƙoƙarin mayar da su saniyar ware tun daga lokacin da babban jarumin na Kannywood ya samu muƙamin babban ofishi a NFC.
Sun ce, sanannen abu ne cewa duk lokacin da NFC ta shirya wani taro ko wani muhimmin al’amari, ba a tuntuɓa ko neman su da sunan bada gudumuwa, inda daga ciki akwai taron baje kolin fina-finai na Zuma Festival da aka yi a kwanan nan.
Sun bayyana cewa, a baya idan za a yi taro irin wannan, to a kan gayyace su musamman ganin yadda suke da tasiri a harkokin fina-finai na arewacin Nijeriya.
Don haka suka ce lallai ba su da nufin sukar kowane mutum, saidai sun yi bayani ne domin sauke nauyi a matsayinsu na jagorori, sannan kuma da neman hukumar NFC ta yi nazari akan abinda aka faɗa akanta tare da ɗaukar matakan da suka dace musamman ganin yadda ƙungiyoyin suke da muhimmanci wajen gudanar da harkokinta.
