Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyoyin masana’antun fim na Arewa biyu – Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN) da Arewa Filmmakers Association of Nigeria (AFMAN) – sun aika wasiƙar ƙorafi zuwa ga Hukumar Film ta ƙasa (NFC), suna zargin cewa an ware su daga muhimman shirye-shiryen gwamnati da ke da nasaba da masana’antar fina-finai.
A cikin wasiƙar da shugabannin ƙungiyoyin biyu suka rattaba hannu, sun nuna matuƙar damuwa da cewa tun bayan zuwan sabon shugabancin NFC an samu gurbacewar hulɗa, rashin ganawa da juna, tare da abin da suka kira nuni da wariyar cin zarafi ga masana’antar fim ta Arewa.
Kungiyoyin sun ce kafin zuwan sabon shugabanci, NFC na gudanar da kyakkyawar mu’amala da su ta fuskar haɗin gwiwa, tallafawa ƙarin basira, da duk wani mataki da ya shafi inganta harkokin fim a Nijeriya. Amma sun ce yanayin ya canja kwata-kwata a yanzu.
Sun bayyana misalin bikin Zuma Film Festival – babban taron ƙasa da NFC ke shirya wa – inda suka ce babu wata gayyata, magana ko wani irin haɗa kai da aka yi da AFMAN ko MOPPAN, duk da cewa suna daga cikin ginshiƙan masana’antar fim na ƙasa.
ƙungiyoyin sun ce wannan matakin ya nuna gogewar muhimman ƙungiyoyi, tare da aika saƙon da ba shi da daɗi game da yadda ake kallon nagartar Arewa a harkar fina-finai.
A cikin wasiƙar, MOPPAN da AFMAN sun jaddada cewa tabbatar da ci gaban masana’antar fim ya dogara ne da haɗin kai, adalci, da daidaito tsakanin dukkan yankuna. Saboda haka suka ce rashin saka su a muhimman shirye-shirye ya saɓa wa manufar ƙasa ɗaya mai haɗin kai.
ƙungiyoyin sun buƙaci NFC da ta sake duba matsayinta, ta dawo da ƙulla alaƙa da ƙungiyoyin Arewa domin gina amincewa da haɗin kai. Sun kuma nuna cewa Kannywood tana da babbar rawar da take takawa wajen tattalin arzikin al’adu a Nijeriya, saboda haka kamata ya yi a mutunta su kamar sauran ƙungiyoyin ƙasar.
A ƙarshe, shugabannin ƙungiyoyin biyu – Shehu Hassan Kano na MOPPAN da Salisu Mohammed Officer na AFMAN – sun ce suna buɗe ga tattaunawa, tare da fatan hukumomi za su mayar da hankali cikin gaggawa.
