Za a fara sayer da fetur a N739 ranar Talata, inji Ɗangote

Spread the love

Kamfanin mai na Ɗangote ya sanar cewa daga ranar Talata, 17 ga Disamba, 2025, za a fara sayar da man fetur (Premium Motor Spirit – PMS) a gidajan mai da ke hulɗa da kamfanin a faɗin ƙasar nan kan farashin N739 kowace lita.

Wannan sauyi ne mai muhimmanci a ɓangaren man fetur na ƙasa, yayin da aka fara amfani da man da aka tace a cikin gida daga matatar Dangote, wanda zai iya rage dogaro da shigo da mai daga waje.

Masana harkar suna ganin wannan ci gaba zai iya rage matsin lamba a kasuwa tare da daidaita farashin mai a nan gaba.

By Babaji