
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An samu ɓullar sababbin jawabai na Fadar Shugaban Ƙasa a zamanin mulkin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yayin da ƴarsa Fatima Buhari ta ce marigayin ya koma karɓar magana daga gare su a rubuce saboda tsoron bayyanar sirri.
An samu wannan jawabin ne a wani sabon littafi mai suna “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari”, da Dakta Charles Omole, Shugaban Cibiyar binciken tsare-tsaren ƴan sanda da tsaro ya wallafa.
An ƙaddamar da littafi ne a Abuja a ranar Litinin a Fadar shugaban ƙasa, wanda ya ƙunshi tarihin rayuwar marigayi Muhammadu Buhari.
A cewar Fatima, an yi wani lokaci da Buhari yake zargin an dasa waɗansu na’urorin ɗaukar sauti a ofishinsa na fadar, lamarin da ya tilasta musu yin magana da shi ta wani salo da ba a saba ba, wato ta hanyar rubutu.
Ta kuma ce, duk lokacin da ak wani zama, Buhari ya kan ƙaurace wa yin magana da baki, a madadin haka saidai ya zaɓi ya riƙa rubutawa da yin alama da hannu don kada a ji a inda bai dace ba.
Fatima ta ƙara da cewa, mahaifin nasu ya sha gargaɗin ta a kodayaushe akan ta riƙa kula sosai saboda shi ma yana cikin kulawar jami’ai a kodayaushe duk da cewa shi ne shugaban ƙasa.
Kazalika, ta ƙalubalanci yadda ake samun irin haka a fadar mai cike da tsaro, tana mai kokawa game da amfanin tasirin ƴan gaba-gaba na gwamnatin.
