
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Hukumar kula da Harkokin Man fetur da Rarrabawa ta ƙasa (NMDPRA), Injiniya Farouk Ahmed ya nesanta kansa daga zargin rashawa da ya karaɗe kafafen watsa labarai da Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, wato Alhaji Aliko Ɗangote ya yi akan sa.
A wani saƙo da ya fitar wa manema labarai a yau Laraba, Ahmed ya musanta yin tsokaci akan zarge-zargen, wanda aka yi ta yaɗawa a kafafen sadarwa, yana mai bayyana hakan a matsayin ƙarya kuma abin da ba da yawunsa ba.
Hakan na zuwa ne yayin da al’umma ke cigaba da cece-kuce akan kalaman Ɗangote na ranar Lahadi a Lekki ta Jihar Legas, inda attajirin ya nemi hukumomi da su yi bincike akan inda da yadda shugaban na NMDPRA ya samu kuɗin da ya tura ƴaƴansa karatu a ƙasashen waje.
Ɗangote dai ya yi zargin Ahmed da kashe jimillar Dala miliyan 5 akan ilimin sakandare na ƴaƴansa huɗu a makarantun ƙasar Switzerland na tsawon shekaru shida, lamarin da ya bayyana a matsayin abin da ya saɓa wa matakin kuɗin shiga na jami’in gwamnati.
Akan haka ne ya yi kira ga Ahmed da ya je gaban kwamitin shari’a na CCT domin bada ba’asin kadarorin da ya mallaka da yadda yake gudanar da lamuran kuɗaɗensa.
Haka kuma, Ɗangote ya tabbatar da shigar wa Hukumar Yaƙi da Rashawa da Manyan Laifuka (ICPC) ƙorafi akan lamarin tare da neman ta yi bincike a kai.
A jawabinsa na ranar Talata, Farouk Ahmed ya musanta yin tsokaci akan al’amarin a bainar jama’a, yana mai cewa ya yi hakan ne bisa ganin damansa da tsare mutuncin ofishinsa.
