NNPC ya ƙaddamar da bincike bayan fashewar bututun gas na Escravos–Legas

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An shiga fargaba a sassan ƙasar nan bayan wata mummunar fashewa da ta afku a kan bututun iskar gas na Escravos–Legas, wanda ke daga cikin muhimman ginshiƙan tsarin samar da lantarki a Nijeriya.

Kamfanin NNPC ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a daren Juma’a, inda ya bayyana cewa fashewar ta janyo katsewar iskar gas tare da tayar da gagarumin matakin gaggawa domin daƙile illar da ka iya biyo baya.

A cewar kamfanin, fashewar ta faru ne a kusa da yankin Tebijor, Okpele da Ikpopo da ke yankin Kudu maso Yammacin Warri a Jihar Delta.

Injiniyoyin da ke sa ido kan tsarin sun gano babbar matsala a cikin bututun, abin da ke nuna yiyuwar fashewa ko zubewar iskar gas, lamarin da ya sa aka rufe layin baki ɗaya domin kariya.

Ko da yake NNPC bai bayyana cikakkun bayanai kan girman ɓarnar da aka samu ko an rasa rayuka ba, lamarin ya tayar da hankula matuƙa game da yiwuwar tasirinsa kan samar da wutar lantarki da kuma iskar gas ga masana’antu, musamman a yankunan Kudu maso Yamma da ke dogaro sosai da wannan bututu.

Bututun Escravos–Legas na da ikon jigilar kusan cubic biliyan 2.2 na iskar gas a kowace rana, kuma shi ne jigon ciyar da manyan tashoshin wutar lantarki irin su Egbin, Omotosho da Geregu, baya ga wasu manyan masana’antu. 

Tarihi ya nuna cewa duk lokacin da aka samu matsala a kan wannan layi, wutar lantarki a ƙasar na shiga matsanancin ƙunci, lamarin da ke ƙara tsananta matsalar ƙarancin wuta da Nijeriya ke fama da ita.

NNPC ta ce, an ƙaddamar da cikakken bincike domin gano musabbabin fashewar. Haka kuma, an tura tawagogin gaggawa na kamfanin tare da jami’an tsaro da shugabannin al’umma domin killace yankin, tabbatar da tsaro da kuma hana ɓarkewar wata matsala ta gaba.

“Mun haɗa kai da dukkan hukumomin da abin ya shafa tare da al’ummomin yankin domin rage illar da lamarin ka iya haifarwa,” inji NNPC, wadda ta ƙara da cewa za a ƙara ƙaimi wajen gyare-gyare da dawo da aiki da zarar an kammala tantance tsaro.

Har yanzu hukumomi ba su tabbatar ko fashewar ta samo asali ne daga lalata, matsalar kayan aiki ko wani haɗari ba, yayin da jama’a da masana ke jiran karin bayani kan yadda lamarin zai shafi samar da wutar lantarki a ƙasar.

By ukarofi