Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
’Yan sandan Nijeriya sun sanar da cewa za su ci gaba da tilasta bin dokar mallakar lasisin amfani da gilashin mota mai duhu ko kuma su ci gaba da kame daga 2 ga Janairu 2026, abin da ya janyo suka daga ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA), wadda ta bayyana matakin a matsayin saɓa wa hukuncin kotu da kuma tauye doka.
Wannan sanarwa ta fito ne daga CSP Benjamin Hundeyin, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ‘yan Sanda, a ranar 15 ga Disamba 2025.
NBA ta bayyana cewa matakin ’yan sandan ya saɓa wa hukuncin da kotu ta yanke inda ta dakatar da aiwatar da dokar har sai an gama shari’ar ƙarar ’yan sandanda aka shigar a gabanta na ƙalubalantar halaccin dokar.
Lauyoyi sun yi gargaɗi cewa wannan mataki zai ƙara nauyi ne ga talakawa, kuma zai iya jawo cin hanci da rashawa.
Wannan lamarin ya fara ne a watan Afrilu 2025 lokacin da rundunar ’yan sandan Nijeriya ta shigo da dokar mallakar lasisin gilashin mota mai duhu, wacce ta buƙaci ‘yan Nijeriya su yi rijista ta intanet domin samun lasisi inda aka tsara fara aiwatar da dokar a ranar 1 ga Yuni 2025, daga baya aka ɗage zuwa 2 ga Oktoba saboda ƙorafe-ƙorafe da dama daga jama’a.
NBA ta buƙaci ’yan sandan da su dakatar da duk wani mataki na ci gaba da aiwatar da dokar har sai kotu ta yanke hukunci na ƙarshe.
