Yadda shugaban CAC ya mallaki gidajen miliyan N700 cikin shekara biyu — Rahoto

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rahoton bincike da kafar yaɗa labarai ta SaharaReporters ta wallafa ya tona zargin yadda Shugaban Hukumar Rajistar Kamfanoni ta ƙasa (CAC), Ishaƙ Hussaini Magaji (SAN), ya mallaki dukiya mai yawa da ta haɗa da gidajen alfarma guda biyu a birnin Abuja, duk kuwa da cewa albashinsa na wata bai wuce naira dubu 583 ba.

Majiyoyi da dama sun bayyana cewa Magaji, cikin ƙasa da shekaru biyu da karɓar muƙamin sa a shekarar 2023, ya sayi gidaje guda biyu a unguwar Jahi, kowanne na kusan Naira miliyan 350.

Rahoton ya ƙara da cewa, kayan ɗaki da na’urorin da aka girke a gidajen sun zarce darajar gidajen da kansu, abin da ya ƙara haifar da tambayoyi kan tushen kuɗaɗen.

Kafin naɗjn nasa a matsayin shugaba, rahoton ya ce Magaji na zaune ne a wani gidan haya mai ɗakuna uku a Redbricks Estate da ke Katampe Road, inda ake cewa yana fuskantar matsala wajen biyan kuɗin hayar Naira miliyan biyu. Sai dai cikin ɗan lokaci bayan samun muƙamin, an ce ya koma mallakar gidajen alfarma guda biyu da kamfanin Interactiɓe Property Development Company ya gina.

Majiyoyi sun ce kowanne gida an sanya masa tsarin wutar lantarki ta hasken rana da aka shigo da shi daga Jamus wanda darajarsa ta kai Naira miliyan 70, tare da kayan motsa jiki daga China da suka kai Naira miliyan 50. Haka kuma, an ce kowanne gida na da ɗakin sinima mai hana amo shiga ko fita.

Rahoton ya ambato wata majiya da ta bayyana cewa Magaji na da alaƙa da wasu mutane da suka taimaka masa wajen samun muƙamin, inda aka yi iƙirarin cewa ya yi alƙawarin amfanar da kowa, sai dai daga baya ya yi watsi da wasu daga cikinsu. An ce har ya saya wa mahaifiyarsa wani gida mai ɗakuna uku a Abuja bayan ya ɗauko ta daga Jos.

Dangane da wajibcin dokar bayyana kadarori, rahoton ya ce ana zargin Magaji da jinkirta cika takardar bayyana dukiyarsa a Hukumar Kula da ɗa’a (Code of Conduct Bureau) domin ya fara sayen gidajen, sannan daga baya ya bayyana su a matsayin dukiyar da ya riga ya mallaka, abin da ake cewa ya saɓa wa ƙa’idojin aiki ga jami’an gwamnati.

Rahoton ya kuma ce Magaji ya mallaki motocin alfarma masu tsada, ciki har da wata mota da aka ce ta kai darajar miliyoyin daloli, da kuma wata Leɗus Lɗ 600 da aka ce darajarta ta haura Naira miliyan 400.

Takardun albashi da SaharaReporters ta ce ta samu sun nuna cewa a shekarar 2023, albashin Magaji bayan cire haraji ya kasance Naira 546,186.66, yayin da a 2024 ya kai Naira 583,333.33. Takardar naɗin sa, wadda Bola Ahmed Tinubu ya amince da ita, ta nuna cewa an naɗa shi ne a matsayin Shugaban CAC daga 12 ga Oktoba, 2023, na tsawon shekaru huɗu.

Zargin ya sake tayar da muhawara a ƙasar kan yadda jami’an gwamnati ke tara dukiya cikin ƙanƙanin lokaci, da kuma buƙatar hukumomi su binciki gaskiyar waɗannan iƙirari domin kare amincewar jama’a.

By ukarofi