Neja: Iyaye sun roƙi gwamnati ta ceto ’ya’yansu kafin Kirsimeti

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Iyaye da ‘yan uwan ɗaliban makarantar Katolika da aka sace a ƙaramar hukumar Agwara ta jihar Neja sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatin jihar Neja da su gaggauta ceto sauran ‘ya’yansu da har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutane.

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa yaran sun shafe makonni a daji suna rayuwa cikin mawuyacin hali, inda ake ba su tuwon gero da miyan kuka sau ɗaya kacal a rana, tare da shan ruwa mai datti.

Lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Nuwamba 2025, lokacin da aka sace ɗalibai 303 da malamai 12 daga makarantar St. Mary’s a Agwara.

Da farko an ruwaito cewa ɗalibai kusan 215 ne aka tafi da su, amma daga bisani wani ƙirga ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) ta yi ya tabbatar da cewa adadin ya fi haka.

Rahotanni sun nuna cewa ɗalibai 50 sun samu damar tserewa a farkon kwanakin sacewar, yayin da gwamnati ta samu nasarar kuɓutar da ƙarin ɗalibai 100. Waɗanda aka ceto sun haɗu da iyayensu makon da ya gabata cikin yanayi na hawaye da farin ciki, tare da fargaba kan makomar sauran da ke tsare a daji. A halin da ake ciki yanzu, aƙalla dalibai 153 tare da dukkan malamai 12 na nan a hannun masu garkuwa.

Gwamnatin tarayya ta bayyana tausayinta ga iyayen, tare da ba su tabbacin cewa tana aiki tuƙuru domin ganin an kubutar da sauran ɗaliban. Sai dai iyayen sun ce lokaci na wucewa yana ƙara musu raɗaɗi, musamman ganin halin wahala da ‘ya’yan ke ciki.

Dauda Shikolo, ɗaya daga cikin iyayen da aka saki ɗansa, ya ce ko da yake yana jin daɗi da dawowar yaron, akwai iyalai da dama da har yanzu ke kuka saboda ‘ya’yansu na nan a daji. Ya roƙi gwamnatin tarayya da ta jihar Nijar da su yi duk mai yiwuwa wajen ceto ragowar yaran kafin Kirsimeti. A cewarsa, yaran sun sha wahala a daji mai cike da sauro, inda ake ba su kaɗan daga tuwo da miya, suna kuma shan ruwan laka.

Wani mahaifi, Fasto Ayuba, ya bayyana halin da yake ciki a matsayin haɗuwar farin ciki da baƙin ciki. Ya ce an sace ‘ya’yansa biyu, amma ɗaya daga cikinsu na cikin wadanda aka ceto. Ya ce yana addu’a sosai domin ganin an kuɓutar da zayan da ke tsare, tare da sauran yaran, domin iyalansu su yi Kirsimeti cikin haɗin kai.

Ya kuma nuna damuwa cewa wasu daga cikin yaran na fama da rashin lafiya, yana mai rokon gwamnati da kada ta yi jinkiri wajen ɗaukar mataki.

A wani ɓangare, rundunar sojin ƙasa ta sanar da karɓar sabbin sojoji 3,439 da aka horas a sansanin horarwa na sojoji da ke Zariya, domin ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro. Da yake jawabi a wajen bikin fitar da rundunar ɗaukar horo ta 89 a filin Hamma Kin Parade Ground, Babban Hafsan Sojin Kasa, Waidi Shuaib, ya gargaɗi sabbin sojojin da su kasance masu ɗabi’a, jarumtaka da biyayya ga ƙasa.

By ukarofi