Zangon ƙarshe na rayuwar Buhari ya kasance cike da jimamin rashe-rashe – Aisha Buhari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Dakta Aisha Buhari ta bayyana shekarar ƙarshe ta rayuwar Buhari a matsayin abin da ya fuskanci yawan jana’iza da tafiye-tafiye akai-akai bayan saukarsa a karagar mulki da tsananin rashin lafiya da ya fuskanta.

Aisha ta bayyana haka ne a littafin “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari”, wanda Dakta Charles Omole ya wallafa, inda ta bada ba’asin kwanakin ƙarshe na tsohon shugaban ƙasar da halin ƙunci da iyalansa suka shiga.

A cewarta, rashin lafiyar Buhari ya tsananta ne a lokacin da ya kammala wa’adinsa biyu na shugabancin Nijeriya, inda aka sanya shi a ɗakin masu dogon suma na tsawon kwanaki da kuma zamansa a sashen kula da marasa lafiya na asibiti.

Ta bayyana kwanaki ukun ƙarshe na rayuwarsa a matsayin lokaci mafi tsananin ƙunci ga iyalansa.

Ta kuma ce, bayan ya sauka daga kujerar mulkin Nijeriya iyalansa sun fuskanci halin mace-macen makusanta da tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje musamman tsakanin Nijeriya da Ingila inda a nan Buhari ke zuwa neman magani.

Matar marigayin shugaban ƙasar ta ƙara da cewa, da fari ya je Ingila domin jinyar haƙori da hutu, inda a lokacin ita kuma tana Abuja wajen jana’izar ɗa a gare ta. Daga bisani ta koma Landon, sannan ta sake dawowa Nijeriya sakamakon rashin wani kawunta.

Har’ilayau, ta jingina sarƙaƙiyar rashin lafiyar marigayin da shekarun tsufa, shekerun fuskantar matsanancin sauyin yanayi a lokacin da yake aikin soja da kuma ƙalubalen rayuwa a baya.

By Babaji