Gwamnatin Kano ta raba wa mata fom don bunƙasa sana’o’insu

Spread the love

Gwamnatin Jihar Kano ta sake raba fom ga mata domin cigaba da tallafa musu wajen bunƙasa harkokinsu na kasuwanci a faɗin jihar.

A sanarwar da Jami’ar Yada Labarai ta Karamar Hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa Manema Labarai, Shugaban Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ne ya bayyana haka, a yayin da Kungiyar Mata masu Sana’ar Man Kuli suka kai masa ziyara a ofishinsa dake sakatariyar karamar hukumar.

Shugaban Majalisar yankin, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ya bayyana jin dadinsa bisa amanar jagororin kungiyar matan masu sana’ar, bisa isar da sakon tallafin da ya yi musu a baya, kasancewar wannan shi ne karo na uku da kungiyar ta sake waiwayensa domin tallafa musu.

“In Sha Allahu za mu ci gaba da bakin kokarinmu na yadda za a ci gaba da tallafa muku, musamman a kan irin wannan sana’ar taku ta matsar man kuli, ga shi har daga wani wajen ana zuwa a kawo muku aiki domin ku matse ku ba su man ku dauki ribarku, wannan ba karamin abin alheri ba ne. Don haka in sha Allahu za mu yi kokari a karamar hukuma mu ga yadda za mu dada taimaka muku a kara muku naira dubu dari uku 300, 000. Da za ku je ku hada a kungiyarku domin bunkasa wannan kasuwanci naku”, inji shi.

Ya ce, akwai abubuwa da dama da gwamnati za ta bijiro da su na tallafa wa harkokin mata da za su ci gaba da inganta rayuwarsu ta fuskar sana’a, bisa la’akari da duk wanda ya taimaki mace tamkar ya taimaki al’uma ne baki daya.

“Yanzu fama-famai da aka ba ku kwanan nan, mai girma Gwamna ya ba da umarni, ana bi ana karba za a je a kawo kiwace mai fam za a damka mata jarin naira dubu hamsin 50, 000.” In ji shi.

Da take jawabi, Shugabar kungiyar, Malama Hauwa Abdullahi Buden Waje, ta jinjina wa Shugaban yankin bisa tagomashin da ya yi musu a baya, kasancewar a wannan karon sun je ne domin ya taimake su su tsaya da kafafunsu, sakamakon kwarewa da suke da ita wadda ta kai gejin da za su iya koyar da wasu.

Jami’ar Hulda da Jama’a ta kungiyar kuma Shugabar Akwatin Buden Waje, Malama Wali Musa, ta gode wa shugaban karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, tare da yaba wa dukan jagororinsu da suka zama tushen mafarin wannan sana’a tasu, wadanda suka hada da; Malam Sa’idu Nabarda, Shugaban Akwatunan Buden waje, da ya yi magana a madadinsu.

“Ba ‘Yan Buden Waje ba, a yanzu, har daga wajen Bichi akwai wadanda suke zuwa a kan su hada gwiwa da su sakamakon ganin yadda harkokin kasuwancinsu yake gudana. Gyadar da suke amfani da ita mafi yawa idan sun dauko sai sun sayar suke kai kudin. Alhamdu Lillah kowa ya san mahimmancin gyada da kuli a Jihar Kano yadda suke ba da gudunmawa, a Karamar Hukumar Bichi muna kiranka da in ka rike mana wadannan matan in sha Allahu sai ya zama tamkar wani kamfani ne da sunan Alhaji Hamza Sule Mai Fata da zai kasance ana fatar da kuli da mai”, inji shi.

By Babaji