DAGA JOHN D. WADA a Lafiya
Manoma a Jihar Nasarawa sunce a yanzu haka suna sa ran samun girbi mai matuƙar amfani saboda gwamnatin Nasarawa ta ce za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen din din din na shirin nan na musamman da aka ƙirƙiro don bunƙasar ayyukan noma a jihar dama ƙasa baki ɗaya wato FG/IFAD-VCDP a turance har bayan shekarar badi ta 2026 ma don cigaba da bunƙasar harkokin noma a jihar baki ɗaya.
Manoman sun bayyana haka ne a wajen wani taron kwana ɗaya na ƙara wa juna sani da aka shirya wa masu ruwa da tsaki a harkar ta bunƙasar ayyukan noma wato Value Change Development Program (VCDP)a turance a birnin Lafiya fadar gwamnatin jihar inda suka jaddada cewar zuwa yanzu horor VCDP din na musamman da suke samu yana cigaba da basu damar bunƙasar amfanin gonakin nasu.
Da yake jawabi a wajen zaman, kwamishinan noma na jihar Nasarawa Honorabul Tanko Tunga, ya ce gwamnatin jihar za ta cigaba da gudanar da shirye-shiryen mayar da shirin VCDP din ta din din a jihar ne saboda tabbas kawo yanzu ta gano hakan yana cigaba da aifar da ɗa mai ido wa manoman jihar gaba ɗaya.
Ya ce, “Za mu yi komai da komai don tabbatar mun cigaba da aiwatar da shirin VCDP ɗin a jihar nan namu na Nasarawa har bayan shekarar 2026 don mun riga mun yanke shawarar cewa shirin VCDP ba zai tsaya a 2026 ba saboda mahimmancinsa ga manoman mu.
“Tabbas zamu iya samun rauni da fuskantar wasu ƙalubalai har na tsawon shekara guda a yayin aiwatar da shirin, amma zamu cigaba da ita.” Inji shi.
Itama a jawabinta na maraba, kodinetan VCDP, Dr. Eunice Adgidzi ta ce shirin na mayar da VCDP din din din a jihar ba shakka zai taimakawa manoma a jihar matuƙa musamman a fannin na wadatattun girbi masu amfani da hakan zai kuma bunƙasa tattalin arzikin jihar da ƙasa baki ɗaya.
Haka shima ɗan majalisar dokokin jihar dake wakiltar mazabar Obi Dr. Peter Akwe, wanda shi ne kuma shugaban kwamitin harkokin noma a majalisar, ya ce ba ja shirin VCDP ya taimakawa manoman jihar kuma zai cigaba da taimaka musu muddin ana cigaba da aiwatar da shi yadda ya dace inda yayi alƙawarin cewa a nasa ɓangaren zai cigaba da yin duka mai yuwa ta kwamitin nasa don tabbatar da nasarar shirin a yankinsa dama jihar baki ɗaya.
A ƙarshe sai Mr. Samson Jonath, wanda shi ne shugaban fannin sanin makaman aiki na shirin baki ɗaya wato Knowledge Management Communication Officer a turance, ya sanar cewa kawo yanzu VCDP ya horar da manoma 62 waɗanda suka amfana da horor yadda ake sarrafa takin zamani na noman shinkafa da na rogo da dai sauran su don cigaba da samun girbi nagari a harkar nomansu kana ya ƙara da cewa kimanin manoman guda 393 ne suka kuma amfana da wani tallafin shinkafar premium da na rogo a ƙananan hukumomi biyar a jihar duk ta shirin.
