Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU a Jos
Gwamnatin Jihar Filato ta bai wa masu gudanar da sana’ar tuƙin babur mai ƙafa uku, da aka fi sani da Keke Napep, tallafin Naira Miliyan huɗu, ƙarƙashin wata ƙungiyar masu taimakawa matuƙa babura ta United People Association of Keke Napep Riders, domin ƙara taimaka musu su samu sauƙin gudanar da sana’arsu.
Jagoran ƙungiyar mai kula da harkokin tallafawa masu baburan, Malam Anas Abubakar Maihali shi ne ya sanar da haka a yayin wani taro da ƙungiyar ta kira, don raba wa wasu masu Keken da suka samu nasara da bashin Naira dubu ɗari, wanda za su biya ba tare da ƙarin ko kwabo ba.
Ya ce, ƙungiyar ta samu tallafin kuɗin ne daga Gwamnatin Jihar Filato ƙarƙashin Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang, wanda ya ba su Naira Miliyan huɗu domin taimakawa mambobinsu, yayin da ɗan Majalisar Dokoki ta Jihar Filato mai wakiltar Arewacin Jos ta Arewa, Dr Adamu Aliyu ya ba da gudummawar Naira Miliyan ɗaya, sai tsohon ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya, Dachung Musa Bagos, da shi ma ya ba da gudummawar Naira Miliyan ɗaya.
Shugaban Kwamitin Amintattu na ƙungiyar, Alhaji Ibrahim Ahmad ya bayyana cewa, an samo wannan tallafi ne domin taimakawa matuƙa baburan Keke Napep, yadda za su iya magance wasu matsaloli da suke fuskanta, sakamakon gazawar ƙungiyoyin masu Keke da ake da su, wajen share hawayen mambobin su.
A cewarsa, sau da dama damuwar kuɗi ta dubu goma zuwa ashirin tana iya sa mai aikin keke cikin matsalar da zai kasa warware wa, sai ya nemi bashi daga wani waje. Don haka aka kafa ƙungiyar a 2015, domin ba da gudummawa ga waɗannan matasa, masu neman halalinsu.
Shugaban riƙon ƙwarya na ƙungiyar Markus Adamu ya bayyana cewa, an raba Naira dubu 500 ga shiyyoyi bakwai dake Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, inda a kowacce shiyya za a bai wa mutane biyar dubu ɗari kowanne su. Bisa tsarin da aka yi, a cewarsa, za a mayar da kuɗin a sati goma ne, yadda a kowanne sati mai Keke zai biya Naira dubu 10, har ya gama biya, ba tare da ya ƙara komai a kai ba.
A jawabinsa, ɗan Majalisar Dokoki ta Jihar Filato, Dr Adamu Aliyu, wanda yana daga cikin mutanen da suka kafa ƙungiyar tun a matakin farko, kafin a zaɓe shi zuwa majalisa, ya yi alƙawarin ganin gwamnatin Jihar Filato ta cigaba da taimakawa ƙungiyar ta hanyoyi daban-daban, musamman ta ɓangaren ba su bashin wasu daga cikin sabbin Keke Napep masu amfani da lantarki da gwamnati ta yi odar kawo su.
Ya shawarci matuƙa baburan da su tabbatar sun yi tattalin kuɗaɗen da aka ba su, don su taimaki kansu da sana’ar su.
A ƙarshen taron, ƙungiyar ta bai wa ɗan majalisar Dr Adamu Aliyu shaidar karramawa, sakamakon gudummawar da yake ba su tsawon shekaru.
