Kano: Ƙaramar Hukumar Bichi ta yi namijin ƙoƙari a allurar rigakafi, inji Mahmud Garba

Spread the love

Sama da yara 92,760 ‘yan kasa da shekaru biyar ne aka yi nasarar yi wa allurar rigakafin cutar shan-inna a Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano.

Jami’in gudanar da allurar rigakafi na yankin, Malam Mahmud Garba ne ya bayyana haka, yayin tattaunawarsu da Jami’ar Yada Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo.

Malam Mahmud Garba da ya gamsu da haka, ya tabbatar da taimakon Allah tare da kokarin Gwamnatin jiha da na Majalisar karamar hukumar suka samu nasarar aiwatar da aikin rigakafin.

Ya ce, yara kimanin dubu daya da dari takwas da saba’in da daya 1871, aka yi nasarar yi wa, daga cikin irin gidajen da suka iske ba sa nan; wadanda suka kunshi yara kimanin 1876, a yayin da suka koma.

Ya bayyana cewa, sun fuskanci kalubale na iyaye da ba su bari an yi wa ‘ya’yansu ba, wanda suka shafi yara dari tara da arba’in da uku, inda daga baya kuma suka samu nasarar yi wa yara dari tara da talatin da bakwai 937.

“An ba mu allurar maganin rigakafi daga jiha guda dubu dari da uku da dari biyu da hamsin 103, 250. Kuma mun yi amfani da ita gaba daya, haka shugaban karamar hukuma ya ba da tallafin alewa da ake ba yara,shi ya sa muka samu damar warware dukkan matsalolin da aka samu.” In ji shi.

Jami’in, ya kuma bayyana cewa wannan aiki na rigakafi, sun aiwatar da shi ne ta hanyar bi gidaje da makarantun firamare da islamiyya, wajen wasan yara, gidan suna, tasha da wajen diban ruwa da sauran guraren da ake tunanin za a samu yara a wajen.

By Babaji