Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Masu Yi Wa ƙasa Hidima ta Nijeriya (NYSC) ta sanar da wani gagarumin sauyi a shirin ta na Koyon Sana’o’i da Harkokin Kasuwanci (SAED), inda ta fito da sabuwar manhaja guda ɗaya da aka daidaita, wadda yanzu ta ƙunshi sabbin dabaru na zamani kamar ilimin ƙirƙirarriyar basira ta AI da ƙirƙirar manhajojin waya, domin ƙarfafa damar aikin yi da kasuwanci ga matasan Nijeriya.
Babban Daraktan NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ne ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki na SAED karo na biyu na shekarar 2025 da aka gudanar a Abuja.
Taken taron shi ne “ƙarfafa Matasa: Gina ƙwarewa Don Guraben Aiki da Kasuwanci Ta Hanyar Haɗin Gwiwa Mai Tasiri.”
Nafiu ya ce, daidaita manhajar SAED wani ɓangare ne na babban tsarin sauya shirin zuwa yanayin fasahar zamani, da nufin tinkarar matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa da kuma tabbatar da cewa kwarewar da ‘yan hidimar ƙasa ke samu ta dace da buƙatun kasuwar aiki ta zamani.
A cewarsa, sabon tsarin horo ya fi mayar da hankali kan kwarewa mai zurfi, mallakar sana’a da fahimtar fasahar zamani, domin ‘yan hidimar su kasance masu gogayya a kasuwar aiki ta duniya da ke saurin sauyawa.
Ya ƙara da cewa, an haɗa ‘yan hidimar ƙasa da shirin Gwamnatin Tarayya na ‘3 Million Technical Talent’ (3MTT), tare da basu damar samun ayyukan nesa na duniya ta kafafen zamani kamar Outsource to Nigeria, NYSC Jobs.ng da SAED SME Toolkit.
Wannan, a cewarsa, zai buɗe musu ƙofa zuwa ayyuka da kasuwanni na cikin gida da na waje.
Nafiu ya bayyana SAED a matsayin ginshiƙin ƙarfafa matasa, inda ya ce sama da ‘yan hidimar ƙasa miliyan 3.18 sun kammala horon kasuwanci da shiryawa aikin yi tun daga 2012.
Haka kuma, ya ce sama da kasuwanni 30,000 da ‘yan hidimar ƙasa suka kafa an yi musu rijista a Hukumar Rajistar Kamfanoni ta ƙasa, lamarin da ke taimakawa samar da ayyukan yi da bunƙasar tattalin arziki.
Babban Daraktan ya kuma jaddada ƙaddamar da asusun rancen MSME na naira biliyan 2 ga ‘yan kasuwar NYSC, a haɗin gwiwa da Bankin Masana’antu, yana mai bayyana hakan a matsayin babban ci gaba a yunƙurin bunƙasa kasuwancin matasa.
Tun da farko, Daraktan SAED, Kehinde Aremu-Cole, ya yaba da gudunmawar abokan hulɗa daga ɓangarori daban-daban kamar fasaha, ƙirƙire-ƙirƙire, noma da ƙarfafa harkokin kuɗi.
Ya ce horo, tallafi da shawarwarin da suke bayarwa na taimakawa wajen gina makomar Nijeriya ta hannun ‘yan hidimar ƙasa, tare da kira da a samar da hanyoyin tallafin kuɗi na musamman domin juya basira zuwa kasuwanci mai ɗorewa.
