Babu mai zuba jari da zai sayi matatun man Nijeriya, inji Dangote

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa yanayin kasuwanci da tsarin doka a Nijeriya ba su dace ba ta yadda ba wani mai zuba jari da zai nuna sha’awar sayen matatun man fetur da Kamfanin NNPC ke da su, ko da gwamnati ta fito da su kasuwa.

Dangote ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya yi a Legas ranar Lahadi, inda ya ce ko a yau NNPC ta yanke shawarar sayar da matatun man, babu wanda zai zo ya saya, saboda yanayin aiki da tsare-tsaren da ke gudana a ɓangaren man fetur ba su ƙarfafa jarin masu zuba jari.

A cewarsa, matsalolin da ke tattare da dokoki, tsari da yanayin kasuwanci sun sanya zuba jari a harkar tace mai ya zama abin guje wa, ba wai ga ‘yan ƙasashen waje kaɗai ba, har ma da ‘yan cikin gida. Ya ce hakan na nufin cewa duk wata magana ta sayar da matatun man gwamnati ba za ta haifar da sakamako ba.

Dangote ya kuma soki gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, yana mai cewa an yi babban kuskure a lokacin da aka bai wa mutum mai sana’ar kasuwanci rawar mai tsara dokoki a ɓangaren mai.

A cewarsa, mai kasuwanci ba zai iya zama mai tsara doka ba, domin hakan na haifar da rikicewar tsari da rashin adalci a tsarin kula da harkar.

Ya ƙara da cewa, wannan kuskure ya taimaka wajen haifar da rikicin da ake fuskanta a yanzu, inda ƙasar ke biyan farashi mai tsada ta fuskar tattalin arziki da ci gaban masana’antu.

Dangote ya jaddada cewa abin da ya fi damunsa shi ne yadda ƙasar ke shan wahala sakamakon wadannan manufofi marasa kyau.

Nijeriya na da manyan matatun man fetur a Fatakwal, Warri da Kaduna, masu ƙarfin tace ganga dubu 445 a rana baki ɗaya. Duk da biliyoyin daloli da gwamnati ta kashe wajen gyara da farfaɗo da su tsawon shekaru, matatun man sun ci gaba da zama marasa aiki, abin da ya ƙara tsananta dogaron shigo da man fetur daga ƙasashen waje.

By ukarofi