Yarjejeniya da Faransa ba za ta raunana tsarin harajin Nijeriya ba – FIRS

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Haraji ta Tarayya (FIRS) ta yi watsi da rahotannin da ke tada ruɗani game da yarjejeniyar haɗin gwiwa (MoU) da ta rattaba hannu da Hukumar Kula da Kuɗin Jama’a ta Faransa (DGFiP), tana mai tabbatar da cewa yarjejeniyar ba za ta yi barazana ga ikon tattalin arziki ko tsaron ƙasa na Nijeriya ba.

A wara wasiƙa da suka aike zuwa Gwamnatin Tarayya, Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai, ƙungiyar Dattawa Arewa (NEF) ta bayyana yarjejeniyar a matsayin haɗari ga tsarin bayanan haraji na ƙasa, tana mai nuna damuwa cewa za a iya fallasa muhimman bayanan tattalin arzikin Nijeriya ga ƙasashen waje.

Amma FIRS ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, yarjejeniyar tana da nufin tallafawa Nijeriya ne wajen gina ƙwarewa da ƙarfafa tsarin haraji, ba tare da bayar da damar shiga bayanan masu biyan haraji ko tsarin dijital na ƙasa ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, yarjejeniyar a duniya ne, kuma manufarsa kawai haɗin gwiwa kan ilimi da horar da ma’aikata ne, ba wai bai wa Faransa damar shiga bayanai ko tsarin Nijeriya ba.

Dukkan dokokin Nijeriya kan tsaron bayanai, tsaron intanet, da ikon ƙasa suna aiki yadda ya kamata.

Yarjejeniyar za ta bai wa Nijeriya damar koyon dabaru da kyawawan tsarin haraji daga Faransa, musamman wajen tsarin fasahar zamani, hidimar masu biyan haraji, da tsara kuɗaɗen jama’a.

Yarjejeniyar ba ta hana kamfanonin fasaha na cikin gida aiki ba; FIRS da NRS za su ci gaba da aiki tare da kamfanoni kamar NIBSS, Interswitch, PayStack, da Flutterwaɓe.

Yarjejeniyar ba ta haɗa da bayar da hidima na fasaha ba; tana mai iyakancewa ga musayar ilimi, ƙarfafa hukumomi, horar da ma’aikata, da bayar da shawarwari kan manufofi da kyawawan ayyuka.

FIRS ta jaddada cewa, maimakon rage ikon ƙasa, wannan yarjejeniyar za ta ƙarfafa shi ne ta hanyar gina hukuma mai zaman kanta, mai kwarewa, da ke iko da tsarin sa, bayanan sa, da dabarun sa.

Hukumar ta bayyana cewa za ta ci gaba da aiki cikin gaskiya, kwarjini, da hadin gwiwa don ci gaban tattalin arzikin Nijeriya a dogon lokaci.

By ukarofi