Matashi ya halaka mutum uku yayin Sallar Asuba a Abuja

Spread the love

Wani matashi ya kashe mutum uku a masallaci a yayin da suke jiran Sallar Asuba a yankin Gwarimpa da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Matashin ya daɓa wa mai kula da masallacin da wasu mutum biyu wuƙa har lahira a yayin da suke jiran sallar ne a masallacin da ke Kado Bimko a shiyyar First Aɓenue da ke shararriyar unguwar.

Wani ganau, Muhammad Auwal, mai shago a kusa da masallacin, ya ce wanda aka fara kashewa, Alhaji Wanzam, dattijo ne da ke sana’ar wanzanci a kusa da masallacin.

“Alhaji Wanzam ya kan zo masallaci tun ƙarfe 4 na Asuba daga gidansa da ke kusa, ya buɗe masallacin, ya tsabtace harabar gaba ɗaya. Yana cikin aikin tsabtacewar ne, sai wanda ake zargi ya kai masa hari, ya yi ta daɓa masa wata sharɓeɓiyar wuƙa,” inji shi.

Muhammad Auwal ya shaida cewa wanda ake zargin, wanda aka fi sani da Laminde Boka, bayan ya kashe Alhaji Wanzam, ya ci gaba da far wa wasu mutane da wuƙar da ke hannunsa.

Laminde Boka, wanda ake kyautata zaton yana cikin mayen miyagun kwayoyi, ya daɓa wa wani mutum da ya yi ƙoƙarin tsayawa ya fuskance shi, wuƙa. Mutumin, wanda ke da injin niƙa a kasuwar da ke kusa, ya rasu a kan hanya yayin da ake ƙoƙarin kai shi asibiti.

Daga bisani, wanda ake zargi ya bi wasu masu ibada, inda ya cimma wani da ya faɗi ƙasa, ya daɓa masa wuƙa har lahira.

A ƙarshe mutane suka ritsa shi a harabar masallacin, suka yi ta jifan sa da duwatsu, kafin daga ƙarshe su buge shi da sanda, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take.

Gawar na uku kuma, wanda birkila ne daga Jihar Gombe, an kai ta ɗakin ajiyar gawa a Asibitin Kubwa a Abuja, saboda ba a samu danginsa ba har zuwa ranar Lahadi, duk da cewa al’umna su san shi a matsayin ma’aikaci.

Wani shaida ya ce an fara jefar da gawar wanda ake zargi a kan bola, kafin daga baya ’yan sanda su kai ta ɗakin ajiyar gawa na Asibitin Kubwa.

By ukarofi