’Yan sanda sun kama magidanci bisa zargin dukan matarsa har lahira

Spread the love

Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta tabbatar da cafke wani mutum mai shekaru 58, ɓitalis Nwoko, ɗan asalin Umuagba da ke ƙaramar hukumar Ahiazu Mbaise, bisa zargin dukan matarsa, Uloma, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Henry Okoye, ya bayyana cewa jami’an ’yan sanda daga sashen Ahiazu Mbaise ne suka kama wanda ake zargin, bayan ’yar uwar mamaciyar ta kai rahoton lamarin ofishin ’yan sanda.

A cewar rahoton, ana zargin Nwoko da yi wa matarsa duka yayin wata saɓani na cikin gida.

Okoye ya ce binciken farko ya nuna cewa rikicin da ya faru a ranar 11 ga watan Disamba ya rikiɗe zuwa faza, inda matar ta faɗi ta suma. Daga bisani aka garzaya da ita asibiti, inda likita ya tabbatar da rasuwarta.

Rundunar ta ƙara da cewa, an miƙa wanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha, SCID, da ke Owerri, domin zurfafa bincike da kuma ɗaukar matakin shari’a da ya dace.

Kakakin rundunar ya ce Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Imo, CP Aboki Danjuma, ya yi kira ga al’umma da su riƙa kai rahoton duk wani lamari na cin zarafin iyali cikin gaggawa. Ya jaddada cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Lamarin cin zarafin cikin gida na ci gaba da zama babbar matsala a Nijeriya, inda mata, maza da yara ke fuskantar barazana a gidaje da dama. Rahotanni sun nuna ƙaruwar irin wazannan laifuka a shekarar 2025, sakamakon matsin tattalin arziki, ɗabi’un al’ada da kuma raunin aiwatar da dokoki. Duk da ƙaruwar jihohin da suka rungumi Dokar Hana Cin Zarafin Jama’a (ɓAPP), ƙalubale na aiwatarwa da tsoron fallasa kansu na ci gaba da hana mutane da dama neman adalci.

By ukarofi