Daga MUKHTAR YAKUBU
An bayyana tsarin boko da kuma Turanci da yake cikin gudanar da bikin’ ‘Kano Indigenous Languages Afrka Film Market and Festival’ (KILAF AWARD) da cewar shi ne yake hana shigar ‘yan Kannywood tsarin wanda mutane suke ganin ‘yan fim ɗin Kannywood ba sa shiga ana damawa da su.Tsohon shugaban ƙungiyar kwararru ta masu shirya fim ta ƙasa MOPPAN Dakta Ahmad Muhammad Sarari ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu dangane da taron KILAF AWARD na wannan shekarar da ya gudana a watan Nuwambar da ya gabata.
Dakta Ahmad Sarari ya fara ne da taya shugaban shirya taron Abdulkarem Muhammad murna da shirya taron inda yake cewa “Ina taya yayana kuma abokina murna taron tun da aka fara ba a tsaya ba, kuma abin kullum yana ƙara haɓaka yana ci gaba, wanda kuma wannan ci gaban ba wai ga mu ‘yan fim ya tsaya ba. Ci gaba ne ga Jihar Kano, Najeriya da ma Afrika baki ɗaya. Don haka tunanin mu ya kamata ya wuce na fim ne kawai saboda shi akwai abubuwa a ƙunshe da shi na ci gaba a rayuwa. Kuma a duk shekara akwai abubuwa na ci gaba na gargajiya da ake yi da na ilimi da koyarwa ta hanyar gabatar da takardu da littattafai, babu shakka wannan abin alfahari ne abin a taya munna ne, kuma mu haɗa hannu wajen ganin cewa wannan abu ya ci gaba.”
A game da rashin ganin ‘yan Kannywood a cikin harkar kuwa Sarari ya ce, “Wato ba baya na ne. Sai dai abin ne tun ran gini tun ran zane. Kuma ita Masana’antar Kannywood ta fim ɗin Hausa ce, kuma komai na Hausa ne . To duk kuma abin da aka ce an kawo Turanci da boko, za ka ga su mutanen mu na Kannywood suna ɗari-ɗari da shi.
Hakika ‘yan kannywood suna zuwa, sai dai a yanzu ana cikin wani yanayin da kowa ya bazama ana aiki, don ko jarumi za ka sa ya yi maka aiki sai ya sa maka lokaci wata ɗaya.
Amma dai magana ta gaskiya su ‘yan Kannywood mafi yawanci ba su karɓi KILAF AWARD yadda ya kamata ba. Dalili shi ne tsari ne da aka yi shi da boko da yawa a cikin sa, da Turanci da yawa a cikinsa. Wannan maganar gaskiya nake faɗa, ba kuma Ina faɗa don na saɓa wa wani ko don wani abu. Ni Ina yabon KILAF AWARD Ina son sa ni ɗan cikin ta ne, tun daga ranar farko ban taɓa fashi ba, ko ba na ƙasar sai na zo an yi da ni, saboda na san wani abin alfahari ne a gare mu da al’ummar Kano da Nijeriya da Afrika gaba ɗaya. Amma na san a hankali ana yin shi ‘yan Kannywood za su juyo. Amma dai su a ɓangaren masu gudanar da KILAF AWARD ɗin ya kamata a ƙara yaɗa sanarwar wajen sanar da jama’a kafin taron ya zo, ta yadda za a tabbatar saƙon ya je wajen kowa.”
