Daga MUKHTAR YAKUBU
A yanzu haka dai shirye-shirye suna fara kankama na bikin ranar Jammaje ta wannan shekarar ta 2025 wanda za a gudanar a ranar 30 ga Disamba a cikin sabuwar Jami’ar Bayero dake Kano.
A wata sanarwa da kwamitin shirya taron ya fitar ta bayyana cewa taron na bana zai kasance na daban ne domin baya ga jawabai da za a saurara daga bakin manyan malamai, to kuma a ranar ne za a haska sabon fim ɗin kamfanin Jammaje Production mai suna ‘Jamila Jammaje’.
Haka nan a wani ɓangare na gudanar da taron za a yi bajekolin litattafai na koyon ilimi a fannoni daban daban.
Sannan kuma za a saurari waƙoƙi daga manyan mawaƙan Kannywood da za su halarci taron domin nishaɗantar da mahalarta taron.
Taron ranar Jammaje dai wani taro ne da shugaban makarantar Jammaje Academy Malam Kabiru Musa Jammaje ya saba shiryawa a duk shekara wanda ɗaliban makarantar daga sassa daban daban na ƙasar nan da sauran jama’a suke halarta saboda yadda ake shirya bikin inda mawaƙa da dama tare da ‘yan fim suke halarta domin nishaɗantar da mahalarta taron.
Ana sa ran dai mawaƙa da ‘yan fim da dama ne za su halarci taron bikin na wannan shekara bayan gabatar da jawabi daga manyan malamai da za a saurara a wajen taron.
