Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kwamishinan ciniki, masana’antu da yawon shaƙatawa na jihar Katsina Hon. Yusuf Rabi’u Jirdede ne ya sanar da hakan yayin taron shugabanin ƙungiyar masu sana’ar ta gwangwan na ƙananan hukumomi 34 dake faɗin jihar katsina.
Kwamishinan ya gabatar masu da kundin dokokin ta hannun lauyan ma’aikatar shari’a Aliyu Isa domin tsaftace masu sana’ar su tare da tantance ya’yan ƙungiyar da irin kallon da wasu jama’a ke yima sana’r tasu.
Hon. Yusuf Rabi’u jirdede ya ƙara da cewa za a buɗe ofis a kowace ƙaramar hukuma domin kula da yadda ake tafiyar da wannan sana’ar ta gwan-gwan.
“Zamu baku dama kowa yayi bayani dangane da wannan ƙudiri na gwamnatin jihar katsina domin tabbatar da tsari da kuma daidaito”.
Shugaban ƙungiyar na jiha Alhaji. Mustapha Sulaiman Rimi ya bayyana jin daɗin su dangane da yadda maigirma gwamna ya tina dasu ya kuma kawo masu gyare-gyare a cikin sana’ar tasu, inda suka tabbatar da goyon bayansu game da wannan ƙudirin doka.
Taron yasamu hallartar kwamishinan Shari’a Fadila Kurfi. Mai ba gwamna shawara kan asusun bai ɗaya Dakta. Salisu Ladan da sauran daraktocin hukumar.
An daɗe ana zargin masu sana’ar kayan gwangwan da sayan wayoyin wutan lantarki da ake zargi na sata ne.
