Gwamna Raɗɗa ya yi ta’aziyar waɗanda aka kashe a harin masallacin Borno

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina kuma shugaban gwamnonin Arewa maso Yamma Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya bayyana matuƙar alhini da jimami kan mummunan harin da aka kai wa masu ibada a wani masallaci a Jihar Borno.

Gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin “hari mai zalunci, marar ma’ana kuma abin Allah-wadai da aka kai wa fararen hula marasa laifi da ke cikin ibada, tare da take tsarkin wuraren ibada,”inji shi.

Ya ce harin ya yi sanadin salwantar rayuka masu daraja tare da jikkata wasu da dama, lamarin da ya jefa iyalai da al’ummomi cikin jimami da makoki.

A cewarsa, “kowace rayuwar da aka rasa a wannan lamari mai tayar da hankali tana wakiltar gida da ke cikin baƙin ciki da kuma al’umma da ta shiga tashin hankali.”

Ya jaddada cewa masallatai, coci-coci, da dukkan wuraren ibada dole ne su kasance wuri na zaman lafiya, tunani da bautar Ubangiji — ba wuraren kai hari ba.

Gwamna Raɗɗa ya ƙara da cewa irin waɗannan ayyukan tashin hankali abin raɗaɗi ne kuma ba za a amince da su ba, yana mai cewa lamarin ya nuna buƙatar ci gaba da tsayin daka a matakin ƙasa wajen yaƙi da ta’addanci da tsauraran aƙidu a kowane irin salo.

Ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi ga ayyukan da suke yi na kare rayukan jama’a da hana sake faruwar irin waɗannan hare-hare, yana mai buƙatarsu da su “ƙara haɗin gwiwa, zurfafa tattara bayanan sirri, tare da tabbatar da an gano tare da hukunta waɗanda ke da hannu a wannan aika-aika.”

Gwamnan ya kuma roƙi ’yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa masu haɗin kai, taka-tsantsan, da goyon bayan ƙoƙarin tsaro, yana mai jaddada cewa haɗin kan ƙasa yana da matuƙar muhimmanci wajen tinkarar masu neman yaɗa tsoro da rarrabuwar kai a faɗin ƙasar.

Gwamna Radda ya sake jaddada ƙudurin haɗin gwiwar gwamnonin Arewa na ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da Gwamnatin Tarayya domin ƙarfafa tsarin tsaro da kare rayuka da dukiyoyi a yankin.

A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Katsina, Gwamna Raɗɗa ya miƙa sakon ta’aziyya ga Gwamna Babagana Umaru Zulum, Gwamnati da al’ummar Jihar Borno, iyalan waɗanda suka rasu, da kuma waɗanda suka jikkata a harin.

Ya yi addu’ar Allah maɗaukakin sarki ya jiƙansu da rahama, ya bai wa iyalan da suka rasa ransu haƙuri da juriya, kuma ya ba waɗanda ke karɓar magani lafiya cikin gaggawa.

By ukarofi