DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya
Mai neman takarar kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa a inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen 2027 mai zuwa, honorabul Musa Mohammed Maikaya ya yaba wa ƙungiyar al’adun gargajiyar nan na ƙabilar Igbira na ƙasa baki ɗaya da ake kira Shafa Abakpa Community Association (SACA) a turance bisa ƙoƙarin da suke yi wajen cigaba da ɗaukaka al’adun Igbira a jihar Nasarawa dama ƙasa baki ɗaya.
Honorabul Maikaya ya bayyana haka ne a ranar Asabar 27 ga watar Disambar shekarar 2025 da ake ciki a lokacin da ya halarci wani babban bikin ƙungiyar Shafa Abakpa Community Association (SACA) din wadda ake gudanarwa shekara-shekara a ƙauyen Shafa Abakpa dake ƙaramar hukumar Toto a jihar.
Honorabul Mohammed Maikaya ya kuma yaba wa gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule dangane da ƙoƙari na musamman da yake yi tare da haɗin gwiwar shugaban ƙaramar hukumar Toto honorabul Ahmed Baba Yahaya don maido da zaman lafiya a yankin Toto din gaba ɗaya tare da lura cewa, mazauna yankin duka musamman ‘yan kabilar su ta Igbira da na Bassa inda a yanzu suke zama tare don binne duka bambance-bambancen da suka gabata don cigaban yankin.
Ya cigaba da bayyana cewa “Yanzu tabbas zaman lafiya ya dawo ƙaramar hukumar mu ta Toto, kuma mazauna yankin na bada gudummawa sosai a ƙoƙarin inganta cigaban yankin,” Inji shi.
Ɗan takarar kujerar gwamnan a inuwar APC, Muhammed Maikaya har ila yau ya yaba wa duka mutanen Shafa Abakpa saboda girmamawa da suke da shi ga al’adu, wanda yace hakan na inganta cigaban zamantakewa da tattalin arziki ta hanyar haɗin kai a yankin baki ɗaya.
Shima da yake jawabi, shugaban ƙaramar hukumar Toto, honorabul Ahmed Baba Yahaya shima ya yaba da rawar da SACA take takawa wajen inganta haɗin kai da cigaba, yana bayyana cewa taron Irewha ɗin na da matukar muhimmanci wajen inganta al’adu da hadin kai da cigaban yankin.
Ya yi alƙawarin cewa gwamnatin sa zata cigaba da tallafa wa ƙoƙarin ƙungiyar don tabbatar da ɗourewar muhimmin bikin baje-kolin al’adun gargajiyar don hakan zai cigaba da tabbatar da ɗorewar zaman lafiya da al’adu a yankin.
Tun farko a jawabin sa na maraba, shugaban ƙungiyar Shafa Abakpa Community Association din na ƙasa da suke shirya bikin a kowanne shekara wato Alhaji Usman Shaba Adams yace suna shirya bikin ne da manufar haɗa kawunan duka al’ummar Igbira da sauran makwabtan su baki daya don idar da sakonnin zaman lafiya tare da nuna wa duniya ire-Iran abubuwan al’jabi dake cikin al’adar Igbira da sauran su kama ya kuma bayyana farin cikin sa dangane da yadda bikin na bana ya ƙayatar inda aka samu ɗinbin jama’a suka halarta.
Ya kuma gode wa duka waɗanda suka bada gudumawa a fannoni dabandaban don samun nasarar bikin na bana tare da yin alƙawarin cewa tabbas na badi mai zuwa a 2026 zai fi na bana.
Sauran manyan baƙi da suka yi jawabi a wajen taron da suka haɗa da sarakunan gargajiyan yankin baki ɗaya ciki har da na al’ummar Bassa da shugaban kwamitin shirye-shirye na bikin wato comr. Sam Israel da sauran su duk suma sun yaba wa hangan nesa da ƙungiyar tayi na cigaba da shirya taron shekara-shekara inda suka buƙaci a cigaba da haɗa kai musamman tsakanin ƙabilun biyu su kuma manta da abubuwa da suka faru kwanakin baya su rungumi juna a zauna tare don bunƙasa da cigaban yankin gaba ɗaya.
Abubuwa da aka gudanar ayayin babban bikin mai ɗinbin tarihi sun hada da baje-kolin wasu al’adun kabilar ta Igbira da suka hada da yadda ake farauta da rawa da rera waƙoki da harbin bindigogi na toka da dai sauran su inda ɗinbin ‘ya’yan zuriyar Igbira ɗin daga ciki da wajen jihar da wasu baki daga wasu ƙabilu daban duk suka halarci bikin don kashe kwarkwatar idanun su.


