
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Lahadi ne Shugaba Bola Tinubu ya bar Jihar Legas inda ya tafi Nahiyar Turai domin cigaba da hutunsa na ƙarshen shekara.
A sanarwar da Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaban zai kuma kai ziyara a hukumance zuwa Abu Dhabi, babban birnin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).
Ya ce, Shugaban UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan ne ya gayyaci Tinubu domin halartar wani taro na mako ɗaya kan ɗorewar ci-gaba na 2026, wanda za a gudanar a farkon Janairun 2026.
Onanuga ya kuma ce, taron na tsawon mako ɗaya, an saba yin sa ne domin haɗa shugabannin gwamnatocin ƙasashe, ƴan kasuwa da kuma al’umma don tattaunawa a taron.
Kazalika, sanarwar ta ce Tinubu zai komo gida Nijeriya ne da zarar an kammala taron.

