An shirya walimar taya mahaddata Alƙur’ani uku a mako guda a Kano

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Malam Ahmad Tijjani Lawan Baƙo Maishunku, wanda aka fi sani da Malam Ahmad Maiturare, ya jagoranci shirya walimar taya murnar ɗalibai uku da suka kammala haddar Alƙur’ani mai girma a makarantar tsangayar Khalifah Sheikh Isyaka Rabiu da ke unguwar Goron Dutse a Kano.

An fara walimar ne a Masallacin Khalifah Isyaka Rabiu a ranar Lahadi, inda malamai, iyaye da al’umma suka halarta domin taya mahaddatan murna da yi musu addu’ar samun albarka da tsoron Allah.

A Lahadi ta biyu kuma aka sake shirya walima ta musamman a gidan Malam Tijjani Lawan Maishunku bayan sallar Azahar, inda aka tanadar da abinci da abubuwan sha domin nuna farin ciki da godiya ga Allah.

Malam Ahmad Maiturare ya bayyana cewa an shirya walimomin ne domin nuna girman darajar Alƙur’ani da kuma ƙarfafa al’umma su rika nuna farin ciki ga duk wanda Allah ya azurta da haddar Littafinsa mai tsarki.

Shi ma babban malami a makarantar, Muhammad Alimul Huda Faruku Abdullahi, ya bayyana cewa makarantar Khalifah Isyaka Rabiu an kafa ta sama da shekaru 35 da suka wuce, kuma ta yaye mahaddata da malamai da dama.

By ukarofi