Gidauniyar zuri’ar Baso ta gudanar da taron tallafa wa zumunci a Kano

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Gidauniyar Zuri’ar Baso (Baso Family Foundation) mai shelkwata a birnin Kano ta gudanar da taron shekara-shekara na tallafa wa juna da ƙarfafa zumunci a tsakanin ‘ya’yan zuri’ar Baso. Taron ya gudana ne a Gidan Tunawa da Marigayi Malam Aminu Kano (Mambayya) da ke unguwar Gwammaja a Kano.

Shugaban zuri’ar Baso na ƙasa, Alhaji Hamza Muhammad, tare da shugaban gidauniyar a Jihar Kano, Alhaji Salisu Ibrahim Yahaya, sun bayyana cewa Baso mutum ne da ya fito daga gidan sarauta amma ba sarauta ba, wanda ya yi ƙaura daga Jamhuriyar Nijar zuwa Kano shekaru da dama da suka wuce, inda zuriyarsa ta bunƙasa zuwa dubban mutane a faɗin Nijeriya .

Sun ce an kafa gidauniyar ne domin ƙarfafa zumunci, fahimtar juna da tallafa wa juna a fannoni kamar ilimi, lafiya, tarbiyya da ci gaban rayuwa, domin cigaban wannan zuriya mai albarka.

Sakataren gidauniyar, Alhaji Muhammad Gali Abdullahi, ya ce zuriyar Baso ta yadu a faɗin ƙasar nan, kuma Allah ya albarkace ta da masana addini, masana ilimin zamani da ‘yan sana’o’i masu amfani ga al’umma. Ya ƙara da cewa an shirya gasar kaci-kaci inda aka raba kyaututtuka kamar atamfofi da sauran kayayyaki masu daraja domin ƙarfafa gwiwa.

Taron ya samu halartar manyan baki ciki har da Farfesa Muhammad Lawan Kuaran Gini, Hajiya Salamatu Lawan, Barrista Abdulaziz Sani Muhammad Kiyaye, Hajiya Fadimatu, Khalid Saidu Atete, da sauran shugabanni da ‘ya’yan zuriyar Baso daga sassa daban-daban.

By ukarofi