Zamfara: Sojoji sun halaka ƴan bindiga da dama da tarwatsa sansanoninsu a Tsafe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun atisayen FANSAR YAMMA na Rundunar Sojin Sama na Nijeriya (NAF) shiyya ta 2, sun yi nasarar ƙaddamar da hare-hare ta sama akan sansanonin ƴan bindiga da ke yankin tsaunin Turba da sansanin Kachalla Dogo Sule a Ƙaramar Hukumar Tsafe da ke Jihar Zamfara.

Kakakin NAF, Air Komodo Ehimen Ejodame ya bayyana haka a wata takarda.

A cewarsa, dakarun sun yi amfani ne da waɗansu bayanai na sirri, lamarin da ya sa aka tura jiragen sama a yankunan.

Ya ce, farmakin farko an ƙaddamar da shi ne a tsaunin na Turba, wanda maɓoya ce ta ƴan bindiga, inda aka tarwatse su da makamansu sakamakon samun wajen da aka hara kai tsaye.

Ya bayyana cewa, bayan kammala atisayen, an gano cewa, hakan ya yi sanadiyyar lalata sansanin da halaka ƴan bindiga masu yawa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da atisayen na ‘AI mission’ na biyu a sansanin Kachalla Dogo Sule, wanda sanannen ɗan bindiga ne da ke jagoran wajen samar da ababen fashewa na IED.

Rundunar ta kuma jaddada ƙoƙarinta na cigaba da aiki da sauran dakarun FANSAN YAMMA wajen daƙile ayyukan ƴan ta’adda da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a Arewa maso Yamma.

By Babaji