
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau ne Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, za ta gurfanar da tsohon Antoni-Janar na ƙasa kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami (SAN) a gaban Mai Shari’a Nwite na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Hakan na zuwa ne bayan da hukumar ta shigar da ƙarar badaƙalar wasu maƙudan kuɗaɗe akan Malami da ɗansa Abdulaziz Malami bisa zargin harkokin kuɗaɗe.
An shigar da tuhume-tuhume guda 16 akan mutane biyu a takarda mai lamba kamar haka: FHC/ABJ/CR/700/2025, inda aka sanya Tarayyar Jamhuriyar Nijeriya a matsayin wadda ta shigar. Haka kuma aka sanya Hajia Bashir Asabe a matsayin mai kariya.
Takardun da aka shigar wa kotu sun yi zargin cewa waɗanda ake tuhuma sun gudanar da wasu kuɗaɗe wajen tura su da da ɓoye su ta hanyar yin wasu haramtattun ayyuka.
Masu binciken sun bankaɗo jimillar Naira biliyan 1.014 da daga wani asusun Bankin Sterling da ke da alaƙa da hada-hadar.
