Daga AISHA ASAS
A tsawon lokaci, rayuwar jarumai ta fi shahara ne a inda hasken fitilu yake, tarukan biki da kuma duk wata sharholiya da ake yi da sunan wayewa. Wannan ne ya sa ba kasafai ka ke iya samun jarumin da ya shahara da bai mayar da hankali kan tara kayan ƙawa da birgewa ba. Wannan kuwa ya zama ɗaya daga cikin ɗabi’un da ake faɗa cikin jerin ababen da ke iya kai fitaccen jarumi ga talauci bayan duniya ta ajiye shi.
Sai dai a ɓangaren shahararren jarumin fim ɗan Ghana, John Dumelo, abin ba haka ba ne, domin ya zaɓi gina hanya mai tabbas a daidai lokacin da yake cikin ganiyar shahara, lokacin da mafi yawan takwarorinsa suke jin kansu a sama, suke ganin sun kai matsayin da za su iya gogayya da kowa, don haka suke ganin ba abinda ya kamance su face rayuwa ta manyan mazaje da ba kowace sana’a ce ya kamata su yi ba, karumin ya zaɓi wata hanya ta dabam, hanya mai wahala amma mai ɗorewa, inda ya juya daga kallon noma a matsayin abin ƙyama, ya rungume ta a matsayin babbar sana’a da take ginshiƙin makomar rayuwarsa.
Tun a shekarun baya, Dumelo ya fara bayyana sha’awarsa ga harkar noma, matakin da daga baya ya kai shi ga kafa Melo Farms, gonar da ta mayar da shi ɗaya daga cikin fitattun jaruman Afirka da ke haɗa shahara da sana’a mai ɗorewa.
Bincike ya tabbatar da cewa, John Dumelo yana noma amfanin gona kamar masara, shinkafa, kayan lambu, tare da bunƙasa wasu fannoni na noma. Gonakinsa sun zama tushen ayyukan yi ga ɗaruruwan mutane, inda shi kansa ya bayyana cewa a duk shekara yana ba da aiki ga mutane tsakanin 300 zuwa 400, musamman matasa.
Masana harkar noma sun bayyana cewa, wannan irin shiga da jarumin ya yi wa sana’ar ta noma ba irin ta jeka na yi ka ba ce, wato kawai zuba jari a kawar da kai ba ko a sanya wasu su jagoranci abin, jarumi Dumelo ya zaɓi ya sanya hannunsa a datti don samun damar amsa sunan manomi na gaske, kuma abin birgewa hakan ta faru ne a daidai lokacin da yake cikin ganiyar shahara. Wannan ne ya bambanta Dumelo da da wasu fitattun mutane da ke kiran noma a baki ba tare da aikatau ba.
“Lokacin da mutum mai shahara ya shiga noma da gaske, ba kawai yana samar da abinci ba ne, yana gina tunanin al’umma ne,” inji wani masanin tattalin arzikin noma a Jami’ar Legon.
A shekarar 2025, gwamnatin Ghana ta naɗa John Dumelo a matsayin Mataimakin Ministan Abinci da Noma. Masu sharhi sun ce wannan naɗin ba wai saboda shahararsa a fim ba ce kawai, ta samo asali ne kan irin gogewarsa ta aiki a gona da kuma fahimtarsa kan ƙalubalen da manoma ke fuskanta.
Masana harkar nishaɗi sun ce harkar fim, duk da muhimmancinta, ba ta da tabbas na dogon lokaci, musamman a ƙasashen Afirka inda babu ingantaccen tsarin inshora ko tanadin ritaya ga jarumai.
“Yawancin jarumai suna kashe shekarunsu a hasken kyamara, amma idan hasken ya dushe, ba su da abin da za su dogara da shi,” inji wani masani kan masana’antar fina-finai a yammacin Afirka.
A cewarsa, matakin Dumelo na shiga noma tun yana kan ganiyarsa ya nuna hikima da hangen nesa, domin noma sana’a ce da ke iya ɗorewa fiye da shahara.
Tambayar da ke yawo a zukatan jama’a ita ce: shin wannan hukunci da John Dumelo ya ɗauka shi ne ya kamata sauran jarumai su ɗauka?
Duba da cewa, ‘gani ga wane ya ishe wane tsoron Allah’. Bai zama ɓoyayyen abu ba yadda masana’antar fim musamman ta Afirka, ko ince Nijeriya ke yiwa jaruman da suka bauta mata ajiyewar budurwar wawa, ta hanyar barinsu ba abin kula da kai yayin da ta yi watsi da su.
Mai karatu zai amince da zance na idan ya ɗan waiwayi baya kan irin neman taimako da manyan jurumai ke yin bankwana da duniya da shi.
Jarumi Mr. Ibu a misali idan mun waiwayi masana’antar fim ta Kudu. Kafin shi da bayanshi mun ga jarumai da yawa da suka jima suna bayar da gudunmawarsu sun nemi taimakon jama’a, ko dai don neman lafiya ko suna neman na abinci.
Idan mun waiwaye Arewa kuwa jarumi Malam Nata’ala kawai zai iya zama babban misali duba da irin shekarun da ya kwashe yana nishaɗantar da ma’abota kallo.
Ba muna ƙoƙarin bayyana noma a matsayin hanya ɗaya kawai da ke samar da makoma mai kyau ga jarumai ba, saidai ƙoƙarin bayyana yin sana’a ga jarumai a matsayin dole. Samun sana’a daidai da ƙarfinka don samun abin dogaro bayan fim.
Domin duk wanda yake sana’a koda ba ta kai shi garin arziki ba, tabbas za ta ajiye shi a tashar rufin asiri.
Ga duk wani jarumi da ya san kansa, ya kamata ya dinga tunanin rayuwa bayan shahara, hakan zai ba shi damar amfani da shahararsa wurin gina kansa ta wata sana’ar da ke da tabbas.
Abin da Dumelo ya yi ya zama kira ga sauran jaruma, wato kira na yin amfani da lokacin da ake da ƙarfi da suna wajen gina makoma, ba mancewa da lokacin da shahara za ta juya ma baya ba.
Rayuwar John Dumelo daga fim zuwa noma na nuni da cewa, shahara ba makoma ba ce, hanya ce da za ka iya amfani da ita don gina makoma. Makomar kuwa tana buƙatar tsari, aiki da hangen nesa. A wannan zamani da yawancin jarumai musamman na Najeriya ke barin duniya da ƙoƙon bara, matakin Dumelo zai iya zama wani kira da zai zaburar da jarumai su farka daga mayen giyar shahara da ke ɗibar su ta kai su inda daga ƙarshe za su yi nadama.
