Daga AISHA ASAS
Kungiyar ƙwararrun Masu Shirya Fina-finai ta Nijeriya (MOPPAN) ta bayyana matuƙar farin cikinta bisa naɗin shahararren daraktan fina-finai, Nasir B. Muhammad, a matsayin ɗaya daga cikin manyan alƙalai a Kaduna Film Festival karo na 9.
A cikin wata takardar taya murna da Babban Sakataren ƙungiyar, Dr. Mohammed Ibrahim Gumel, ya rattaba wa hannu, MOPPAN ta bayyana cewa, babu shakka wannan naɗi ya nuna an “ɗaura ƙwarya a gurbinta”, duba da irin gudunmawar da Nasir B. Muhammad ya bayar a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood tsawon shekaru.
Takardar ta jaddada cewa, Nasir B. Muhammad na daga cikin fitattun masana a harkar fim, inda aka ce kusan babu wani muhimmin mataki ko ci gaba da aka samu a fagen shirya fina-finai da bai taka rawa a cikinsa ba, kai tsaye ko a kaikaice.
“Saka Nasir B. Muhammad cikin manyan alƙalan wannan festival alama ce ta gaskiya da amincewa da ƙwarewa. Lallai a wannan karo, ana sa ran alƙalanci mai cike da adalci, nagarta da gaskiya,” inji takardar.
MOPPAN, ƙarƙashin jagorancin Shugabanta, Alhaji Shehu Hassan Kano, tare da dukkan shugabanni da mambobinta, ta miƙa sakon fatan alheri ga Nasir B. Muhammad, tare da yi masa addu’ar samun nasara a wannan babban nauyi da aka ɗora masa.
Haka kuma, ƙungiyar ta yi addu’ar Allah Ya sa Kaduna Film Festival ya gudana cikin kwanciyar hankali, lafiya da cikakkiyar nasara, tare da zama wani muhimmin mataki na ƙara ɗaukaka harkar fina-finai a Nijeriya baki ɗaya.
