An wayar da kan ‘yan kasuwa a Ƙaramar Hukumar Bichi

Spread the love

Tsohon Ministan Kasuwanci da Masana’atu kuma jagoran Kwankwasiyya na Kano ta Arewa, Alhaji.Ahmad Garba Bichi ya yi alƙawarin gayyato dukkan wanda zai ba da gudunmawa wajen haɓaka kasuwanci a Karamar Hukumar Bichi.

Tsohon Ministan ya yi wannan alƙawari ne lokacin da Kungiyar Kasuwar Zamani ta Bichin ta kai masa ziyara.

Alhaji Ahmad Garba Bichi ya bayyana farin cikinsa na wannan ziyara gami da yaba wa tsarin shugabancin kasuwar, ya kuma yi addu’a da fatan Allah ya yi musu jagora tare da ba su ikon sauke nauyin da ya dora musu.

Haka kuma, ya yaba wa Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Karamar Hukumar Bichi Injiniya, Dakta Abubakar Kabiru Abubakar Bichi, bisa gudanar da ayyukan alheri da na raya kasa, musamman wadanda za su janyo hankalin ‘yan kasuwa daga ko’ina a duniya domin gudanar da kasuwanci a Karamar hukumar.

Alhaji Ahmad Garba Bichi, ya yi alkawarin tuntubar dan majalisar tarayyar wajen cigaba da kokarin kammala aikin kasuwar, musamman bangaren biyan kudin gidajen da za a saya domin fadada kasuwar, da kuma tallafa wa ‘yan kasuwar da jari.

Kazalika, Alh. Garba Bichi wanda ya yi alkawarin yin aiki da kungiyar kasuwar kafada da kafada, ya yi addua da fatan alheri ga ‘yan kasuwar da kasuwar baki daya.

Tun da fari Shugaban Kungiyar ‘Yan kasuwar, Alhaji Abubakar Mazahim Saleh, ya bayyana farin cikinsu bisa yadda jagoran ya tarbe su, inda ya bayyana ziyarar a matsayin girmamawa a matsayinsa na shugaba, jagora, dattijo, abin koyi wanda tarihin yankin ba zai taba mantawa da irin gudunmawar da ya bayar ba, musamman wajen kafa mutane a gurare da dama da kuma wasu bangarori daban-daban.

By ukarofi