Kisan gillar Borgu: ‘Yan bindiga sun halaka 42, sun yi garkuwa da wasu a Neja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Aƙalla mutane 42 ne aka halaka yayin da aka yi garkuwa da wasu da dama ciki har da ɗalibai sakamakon wasu hare-haren ‘yan bindiga a ƙauyukan Agwarra da Borgun Jihar Neja.

Mazauna yankunan sun bayyana cewa an yi ta ƙaddamar da hare-haren tun tsawon sama da mako guda sakamakon rashin jami’an tsaro a yankunan da abin ya shafa.

A cewar wata majiya, “sun ɗaure hannayen mutane 37 ta baya, sannan suka yi musu yankan rago a Kasuwar Daji da ke kusa da Papiri, yayin da aka halaka wasu biyar a ƙauyen Kaima.

Haka kuma, sun yi awon-gaba da mutane da dama ciki har da ɗalibai waɗanda daga cikinsu akwai na makarantar nan ta Papiri, wato St. Mary’s Catholic Primary and Secondary School da ke Agwarra da aka sace mutane ɗalibai da malamai a watan Nuwamba acikinta.

Mazaunan sun bayyana cewa, an cinna wa wata kasuwar ƙauye wuta, inda aka fasa shaguna da sace kayan abinci a yayin da kuma aka yi awon-gaba da wasu mutanen yankin.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, Darakta yaɗa labaran Ɗarikar Katolika na Kontagora, Reberen Stephen Kabirat ya ce maharan sun kuma kai hari akan wasu kayayyaki waɗanda mallakar wata kanisa ne, inda a yayin haka ne limamin cocin ya samu tsere wa garkuwa daga maharan.

Ya bayyana cewa, a yayin haka sun lalata wasu sassan cocin, ɗauke wasu babura biyu da tsabar kuɗi da adadinsa ya kai N200,000 tare da yin awon-gaba da wasu ‘yan ƙauyen ciki har da yara.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar ta hannun Kakakinta, SP Wasiu Abiodun ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce ta samu rahoton a daren Asabar wayewar Lahadi.

Sannan, ya ce jami’an tsaro a tawagar haɗaka sun samu kai ziyara yankunan da al’amarin ya shafa, sannan ana ƙoƙarin ceto mutanen da aka sace da dawo da zaman lafiya.

By ukarofi