Kano: Kwamishinan ‘yan sanda ya yaba wa dakaru bisa murƙushe ‘yan bindiga a sassan jihar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Juma’a ne Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, Ibrahim Bakori tare da tawagar jami’an wasu hukumomin tsaro, sun ziyarci sansanonin jami’an haɗaka na JTF da ke ƙananan hukumomin Tsanyawa da Shanono.

Hakan na zuwa ne bayan nasarorin da jami’an waɗanda suka haɗa da sojoji, ‘yan sanda da DSS suka samu wajen daƙile hare-hare da lalata shirin ‘yan bindiga da dama da ke ƙoƙarin kutse wa jihar a ranar 1 ga watan Junairu.

A sanarwar da Kakakin ‘yan sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce tawagar ta kuma ƙunshi “Brig. Gen. AM Tukur, Brigade Commander, 3-Brigade Nigerian Army Kano; Air Commodore M Sulaiman, Commander, 455 Base Services Group, Nigerian Air Force Kano; the Commissioner of Police, Kano State Police Command, and the Deputy Commandant, Nigerian Navy Logistics College Dawakin Tofa Kano” kamar yadda rubuta.

Yayin jawabinsu, manya jami’an sun jinjina wa dakarun bisa mazantakar da suka nuna waje tabbatar da sadaukar da kai da jarumta ga aikinsu, suna masu cewa wajibi ne a yi aiki tare don ganin an ba Nijeriya kariya a matsayinta na ƙasa ɗaya tilo da al’ummarta suka dogara da ita.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma yi godiya ga dukkan ɓangarorin tsaro da suke bada gudumawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar, tana mai kira ga al’umma da ta cigaba da ba jami’an haɗin kai don ganin an samu ɗorewar haka a yankunanta.

A ƙarshe, ta kirayi jama’a da su cigaba da zama masu kula da al’amuran da ke kai-kawo acikinsu tare da ruwaito mata dukkan wani abin zargi ta lambobi kamar haka; 08032419754, 08123821575, 09029292926, ko kuma ta Manhajar ‘NAF Rescue Me’.

By ukarofi