Yanzu-yanzu: Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su farauto maharan Neja

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu ya umarci Ministan Tsaro, Babban Hafsan Tsaro, manyan hafsashin soji, Sufeto-Janar na na ‘yan sanda da Daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da su farauto tare da kama maharan Kasuwar Daji da ke jihar Neja domin su fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

A ranar Asabar da maraice ne dai wasu mahara suka far wa ƙauyen Kasuwan Daji a Jihar Neja inda suka kashe fiye da mutum 30 tare da sace wasu mata da ƙananan yara da ba a san adadinsu ba gami da ƙone kasuwar da sace kayan abinci.

Cikin wata sanarwa da Kakakin shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya umarci jami’an tsaron da su kuɓutar da mutanen da maharan suka sace.

Sanarwar ta ce ana zargin maharan sun taso ne daga jihohin Sokoto da Zamfara domin guje wa hare-haren da Amurka ta kai musu a jajiberin Kirsimeti.

Haka kuma, Tinubu ya aike da saƙon ta’aziyya ga iyalan mutanen da harin ya rutsa da su, yana mai tabbatar musu da cewa hukumomin tsaro za su ƙarfafa ayyukan cigaba da ba al’umma da dukiyoyinsu kariya musamman a yankunan karkara.

By ukarofi