Sojoji sun kashe ’yan bindiga uku a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Har wala yau sojojin sun jikkata wasu tare da ƙwato babura da makamai a hannun ‘yan bindigan.

Haka kuwa ya biyo bayan samame da suka kai a ƙauyen Karaduwa da ke ƙaramar hukumar Matazu a Jihar Katsina.

Wata majiya ta ruwaito cewa samamen, wanda aka gudanar tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro, an ɗauki tsawon lokaci ana musayar wuta da ’yan bindigar, lamarin da ya tilasta wa sauran daga cikinsu tserewa da raunukan harbin bindiga.

Rahoton ya ƙara da cewa an kama ɗaya daga cikin ’yan bindigar da rai, wanda a halin yanzu yake taimaka wa jami’an tsaro da muhimman bayanai a zurfafa bincike da kuma farautar sauran ’yan ta’addar da ke ɓoye.

Jami’an tsaron sun ƙwato babura guda takwas da kuma makamai iri-iri, waɗanda ake zargin ’yan bindigar ke amfani da su wajen kai hare-hare kan al’ummomin karkara da kuma kauce wa jami’an tsaro.

Jami’an tsaron sun tabbatar da cewa za su ci gaba da kai irin waɗannan samame domin murƙushe ’yan ta’adda da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya.

Duk da rahotannin hare haren yan bindiga a wasu sassan kudancin jihar jifa jifa a kwai alamun samun zaman lafiya a jihar.

By ukarofi