An gudanar da taron ranar Galle na 2026 a Jihar Nasarawa

Spread the love

DAGA JOHN D. WADA a Lafia

Ƙungiyar ƙabilar Eggon da ake kira Eggon Cultural & Development Association (ECDA) a turance reshin Galle a jihar Nasarawa ta gudanar da wani babban taronta na shekara-shekara da ake kira Ranar-Galle na shekarar 2026 da ake ciki.

Babban taron na bana mai taken: Harnessing Galle Hill’s Mineral Wealth: Preserving Culture, Promoting Peace, and Powering Development a turance wadda shine karo na biyar an gudanar da shi ne a makarantar sakandaren Galle da ke Nasarawa-Eggon a jihar a ƙarshen makon da ya gabata.

Da yake jawabin maraba, shugaban ECDA reshen Galle, Alhaji Umar Abdullahi Galle ya marabci duka ‘ya’yan Galle daga sassan ƙasar nan baki ɗaya inda ya bayyana cewa taron ranar Galle ɗin ana shirya shi ne da manufar haɗa kawunan duka al’ummar Galle da abokan zamansu waje guda da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da bunƙasa harkokin al’adunsu tare da bai wa wasu da suke taka mahimmin rawa wajen cigaban ƙasar Galle da al’umma gaba daya lambobin yabo.

Yace taron na bana yana ƙalubalantar ‘ya’yan Galle ne baki ɗaya ba kawai game da batun inganta tattalin arzikin yankin su ba amma har da tabbatar da raya al’adunsu da zaman lafiya da kuma zamantakewa.

Daga nan sai shugaban ECDA reshen Galle din, Alhaji Umar Abdullahi Galle ya gode wa duka waɗanda ke bada gagaruman gudumawa don tabbatar da nasarar taron a kowanne shekara tare da yin alƙawarin na badi zai fi na bana idan Allah ya yarda.

Shi ma da yake jawabi darakta janar na hukumar koyon sana’oi na gwamnatin jihar wanda shine shugaban taron na bana wato Dakta Daniel Ewuga Asele ya yaba wa hangan nesa da al’ummar Galle suka yi na gudanar da taron a kowanne shekara Inda yace tabbas hakan yana haifar da ɗa mai ido idan akayi la’akari da zaman tare da kuma cigaba a duka matakai da ake samu a yankin na Galle ƙarƙashin jagorancin Alhaji Umar Abdullahi Galle zuwa yanzu.

Daga nan sai ya buƙaci sauran ƙabilu su yi koyi da wannan kyakkyawar tunani na ECDA Galle don tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙaramar hukumar Nasarawa-eggon da jihar baki ɗaya.

Sauran manyan baƙi da suka yi jawabi jim kaɗan bayan an basu lambobin yabo na musamman da suka haɗa da shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa-Eggon, Barista iliya IBN Aliyu da wakilin sakataren gwamnatin jihar da wakilin marigayi tsohon shugaban sakandaren Galle da Alhaji Usman Na Saude wato shugaban Nasaude International Mining Company kenan da sauran su duk sun godewa wa ƙungiyar ECDA shiyar Galle ɗin don karramawar da tayi musu da lambobin yabon na musamman inda duk suka kuma yi alƙawarin cigaba da mara musu baya don cimma burinsu na samun cigaba da zaman lafiya a duka matakai a yankin.

Taron dai na bana 2026 wakilin mu ya kuma rubuto cewa ya samu halarci ‘ya’yan Galle daga ciki da wajen jihar da manyan baƙi inda suma mawaƙa da maroka suka nishaɗantar da al’umma.

By ukarofi